Ya bayin Allah! Allah (SWT) Yana kaddara wa bayinSa, fitinu da bakin ciki, amma abin da mumini ya sani dukkan abubuwan da suke gudana a bayan kasa, wadanda Allah (SWT) Yake gudanarwa akwai kudirarSa da hikimarSa a ciki.
Babu wani abu da Allah Yake gudanarwa wanda babu hikima kuma babu wani abu da yake gudana a cikin duniya ba tare da sanin Allah ba.
Allah Ya san duk bin da yake gudana a cikin bayinSa, kuma Allah (SWT) Ya halitta wannan duniya ce don ta zama gidan jarrabawa.
Shi ya sa Yake cewa: “Shi ne Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku ya ga wane ne mafi kyan aiki.”
A wani wurin Ya ce, “Lallai ne Mun sanya abin da yake kanta (kasa) ya zama ado gare ta, don Mu jarrabe ku, cikinku wane ne ya fi kyautata aiki.”
Kuma Allah (SWT) Yana cewa: “Muna jarrabarku da alheri da sharri a matsayin fitina, kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.”
Saboda haka duk abin da yake faruwa a wannan duniya mai dadi da marar dadi, mai daci da mai zaki dukkansu jarrabawa ce daga Allah (SWT).
Kuma Yana yin haka domin Ya gwada bayinSa, Ya dawo da masu rabo zuwa gare Shi. Su komo su rike Shi hannu biyu su nemi taimakonSa.
Allah (SWT) Ya kaddara faruwar haka, shi kuma mumini yana sane da cewa Allah duk Yana yin haka ne domin ya gwada imaninsa da yakininsa ya ga gaskiyar alkawarin da ya rike a tsakaninsa da Shi (Allah), ya ga yadda zai koma gare Shi, ya sakankance cewa babu mai iya ba shi agaji sai Shi.
Hakika Allah Madaukaki a ayoyi da dama Ya ba mu labari cewa duk sa’ar da al’amari ya yi tsanani, to sauki yana nan tafe.
Duk sa’ar da masifu suka rika bibiyar juna daga wannan sai wancan, suka kai kololuwa, to mumini ya sa ran cewa sauki yana nan tafe.
Allah Madaukaki, Ya ba mu labarin Annabawa da suka shiga wani hali na kaka-ni-ka-yi, suka samu turjiya daga al’ummunsu, har ma aka shiga gallaza musu tare da mabiyansu aka yi kokarin kashe su tare da hallaka su, Allah Madaukaki Ya ce, har kamar su debe kauna, sai kuma ga shi nasarar Allah ta zo musu.
Allah Ya ce, “A lokacin da Manzannin suka debe kauna (cewa mutanensu ba za su yi imani ba, sun yi da’awar sun yi kiran amma suna ta gamuwa da turjiya kullum karuwa take yi, saboda haka suka debe kauna, su kuma mutanen da ake kiransu zuwa ga imani sai suka rika karyata azabar Allah tana nan tafe, saboda haka ga shi sun kafirce azabar ba ta zo ba, saboda haka sai suka rika cewa Annabawan karya suka yi musu.
Allah Ya ce saboda haka), “Sai taimakonmu ya zo musu…” Saboda haka za ka ga an shiga matsatsi “Har Annabi da wadanda suka yi imani za su ce “Yaushe ne taimakon Allah zai zo mana.”
Kuma (SWT) Ya gaya mana “Zai sanya sauki a bayan tsanani.” Kuma Ya sake cewa: “Lallai a tare da tsanani akwai wani sauki. Kuma lallai tare da wannan tsananin akwai wani sauki.”
Saboda haka tsanani daya sauki biyu, kuma babu ta yadda za a yi tsanani daya ya rinjayi sauki biyu.
Allah Madaukaki, Ya yi alkawarin zai sanya wa muminai mafita kamar yadda suka ga daukewar ruwan sama suka shiga debe kauna Ubangiji (SWT), sai Ya saukar musu da ruwa.
“Shi ne wanda Yake saukar da ruwa bayan mutane sun debe kauna, kuma Ya yada rahamarSa ko’ina da ina. Shi ne Majibincin bayinSa kuma Sha- Yabo.”
Saboda haka Allah (SWT) Ya gaya mana cewa, kada mu debe kauna daga rahamar Allah, kada mu debe kauna daga samun sauki duk yadda muka ga al’amari ya tsananta.
Bawa ya ci gaba da komawa da addu’a ga Allah, ya cire a zuciyarsa cewa akwai wani mahaluki wanda ba Allah ba, wanda zai iya samar masa sauki, ya samar masa mafita daga abin da yake damunsa.
Ya rika sa wa a ransa cewa, Allah ne kadai zai iya yi masa wannan. To a yayin ne zai ga canji zai ga taimakon Allah ya zo masa.
Allah (SWT) ba Ya son bayi masu yanke kauna, yanke kauna ba dabi’ar mutanen kirki ba ce. Annabi (SAW) ya kasance a cikin Hadisin Abdullahi dan Abbas (RA) wanda Imam Ahmad ya ruwaito, Hadisi ne mai tsawo, wanda Annabi (SAW) ya yi ta wasiyya da nasiha ga Abdullahi dan Abbas tun yana yaro.
A cikin nasihar da yake masa kamar yadda yake a Musnad Imam Ahmad, Annabi (SAW) yake ce masa: “Ka sani duk abin da bawa zai ji ba ya so, to akwai wani alheri.
Tana yiwuwa akwai wani abu wanda ba ku so, ya zo muku, amma kuma ya zamto alheri gare ku.”
Sannan Annabi (SAW) Ya ce, “Nasara tana tare da hakuri. Sannan duk tsanani idan ya zo akwai mafita tare da shi, kuma a tare da tsanani akwai wani sauki.”
Haka ya tabbata a cikin Musnad Imam Ahmad da Sunanu Ibn Maja, Hadisin Abu Razin Ukailin (RA), Annabi (SAW) yana cewa: “Ubangiji Madaukaki Yana yi wa bayinSa dariya ganin yadda suke debe kauna daga rahamarSa, tare da cewa ga canje-canjenSa nan a gabansu a kusa da su.
Wato Allah (SWT) yanzun nan sai ya canja abu daga hali zuwa wani hali, suna ganin yadda Allah Yake caccanja abubuwa, amma kuma sai su debe kauna daga samun rahamarSa, sai su rika debe kauna daga fita daga wata azaba ko wani bala’i da suke ciki.
To shi ne a nan shi wannan sahabin yake cewa “Ya Manzon Allah! Ashe Ubangijinmu Yakan yin dariya?” Annabi (SAW) ya ce da shi: “Na’am, eh, yana yin dariya.”
Sai (mutumin) ya ce, “Wallahi ke nan ba za mu rasa alheri ba daga Ubangijin da Yake yin dariya.”
Wannan yana nuna maka cewa Allah (SWT) Yana tare da bayinSa, kuma ba Ya son ya ga bayinsa sun shiga wani hali da za su ji cewa babu wani sauki da zai sake samuwa.
Don haka su rika sa wa a zukatansu cewa Allah zai kawo musu sauki. Abdullahi dan Abbas (RA) a kan ayar “Lallai a tare da tsanani, akwai wani sauki.” Ya ce, ba yadda za a yi tsanani daya ya rinjayi sauki biyu.
Haka shi ma Alhasnul Basri yake fada, cewa babu ta yadda za a yi tsanani guda daya ya rinjayi sauki guda biyu, saboda Allah Ya maimaita tare da karfafawa: “Lallai a tare da tsanani akwai wani sauki.
Kuma lallai a tare da wannan tsanani akwai wani sauki.” Tsanani na farkon ne aka sake maimaitawa, amma “sauki” na farko da na biyu kowanne zaman kansa yake yi.
Saboda haka “Al’usurTsanani” daya ne, sannan “Alyusur- Sauki” kuma guda biyu ne. To babu yadda za a yi tsanani daya ya rinjayi sauki biyu.
Saboda haka Annabi (SAW) yake nuna wa al’ummarsa cewa su daina fitar da kauna daga samun rahamar Ubangiji.
Allah (SWT) Ya ba mu labarin Annabi Yakubu (AS) yana gaya wa ’ya’yansa bayan shekaru masu yawa sun shude da rabuwarsa da dansa Annabi Yusuf (AS), kuma ya dawo ya rabu da dan uwan Yusuf shekaru da yawa bayan ya rabu da Yusuf (AS) amma duk da haka yake cewa “Ya ’ya’yana! Ku je ku yi bincike game da Yusuf da dan uwansa, kada ku yanke kauna daga rahamar Allah.
Babu mai fitar da kauna daga rahamar Allah, sai wadanda suke kafirai.” Saboda haka duk da wannan dadewa da aka yi Annabi Yakubu (AS) bai fitar da rai ba cewa Allah (SWT) zai kuma sake hada su da dansa Yusuf da kuma dan uwansa Bilyamin wanda ya rasa shi daga baya ba.
To haka ya kamata mumini ya kasance. Akwai hikima da ta sa Ubangiji (SWT) Ya sa, sai idan masifa ta yi tsanani, sannan sai sauki ya zo.
Me ya sa Allah (SWT) Ya yi wannan? Shi ne malamai suke cewa akwai hikima a cikin yin wannan, saboda a cikin aikin Allah babu wanda babu hikima a cikinsa. Akwai abubuwa uku a wannan da suka kamata mu fahimta.