Babban Limamin Masallacin Juma’a na unguwar ’yan majalisu ta Apo da ke Abuja, wanda aka dakatar, Sheikh Nuru Khalid, ya mayar da martani kan dakatarwar da aka yi masa, saboda hudubar da ya yi wacce bisa alama ba ta yi wa gwamnati dadi ba.
A ranar Asabar ce Kwamitin Masallacin, karkashin jagorancin Sanata Sa’idu Dansadau, ya sanar da dakatar da malamin daga limanci, saboda kalamansa a hudubarsa ta sallar Juma’a kan matsalar tsaro, musamman harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
- Ramadan: Wadanne irin abinci ne suka dace a ci lokutan buda-baki da sahur?
- Mece ce makomar siyasar Kwankwaso bayan ficewa daga PDP?
Sheikh Khalid, a cikin martanin nasa dai, ya wallafa wata ayar Alkur’ani, inda ya rubuta: “Allah Shi ne mafi girma. Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so, kuma Ya kwace daga wanda Ya so.”
Hakan dai na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan dakatar da shi daga limancin, inda ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da addu’a.
“Ya Allah, Kai ne mai girma da daukaka, Kai ke ba da mulki ga wanda Ka so, Ka kwace daga wanda Ka so, Ka daukaka wanda Ka so, kuma Ka kaskantar da wanda Ka so. Dukkan alheri a hannunKa yake, Kai ne mai iko a kan komai,” kamar yadda ya wallafa ayar.
‘Dalilin da muka cire shi daga limancin’
Sai dai a cikin wani sako da shugaban kwamitin Masallacin, Sanata Sa’idu Muhammed Dansadau ya fitar ranar Asabar, ya ce sun dakatar da malamin ne daga yin limanci saboda hudubarsa da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a.
Sanarwar ta ce, “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ’yan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.
“An dauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’ ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ’yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.
“Ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da wadanda suka saba wa Allah, da masu zabe da kuma kasa,”
Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta saba wa addinin Islama.
Kazalika, a cikin sanarwar, kwamitin ya nada sabbin lamamai na Masallacin inda Malam Mohammad zai yi tafsiri, yayin da kuma Malam Abdullahi zai jagoranci Juma’a.
Abin da limamin ya ce a hudubar
Rahotanni sun ce a cikin hudubar, malamin ya fadi matakin da ya kamata talakawa su dauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, ta hanyar kin fitowa zabe.
“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda daya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zabe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” inji Sheikh Nuru Khalid a hudubar tasa.
Sai dai bisa ga alama kalaman limamin ba su yi wa mahukunta dadi ba, musamman ta inda ya nuna gazawarsu, da yadda suka ce yana tunzura jama’a kada su fito su yi zabe.
Ko a baya dama dai ya sha jawo hankalin gwamnatoci a hudubobinsa da kuma karatuttukansa kan halin da mutane ke ciki, uwa uba ma kan matsalar tsaro.