✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Nasir Abdul-Muhyi ne sabon Shugaban kungiyar Izala

Shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa (JIBWIS) karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamanta, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir sun amince da nadin…

Shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa (JIBWIS) karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamanta, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir sun amince da nadin Sheikh Muhammad Abdun-Nasir Abdul-Muhyi a matsayin sabon Shugaban Gudanarwa na kasa na kungiyar.
Shi dai Sheikh Abdun-Nasir Abdul-Muhyi kafin wannan nadi, shi ne Mataimakin Shugaban Gunadarwar, kuma ya taba rike Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar reshen Jihar Filato.
Shugabannin kungiyar sun amince da nadin ne, a wajen wani taro na kasa da suka gudanar a garin Tambuwal da ke Jihar Sakkwato, bayan rasuwar tsohon Shugaban Gudanarwar Alhaji Abdurrahaman Marafa Tambuwal a karshen makon jiya.
Shugabannin sun kuma amince da nada Alhaji Hashimu Mai’atamfa Kaduna, a matsayin Mataimakin Shugaban Gudanarwar na daya da Dokta Sani Sa’idu Sagir Sakkwato mataimaki na biyu.
Sai Malam Aliyu Abdullahi Gagare Kaduna a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar da  Alhaji Bala
Adamu Sani Mataimakin Sakatare Janar, sai  Alhaji Idris Malwa Sakataren Gudanar da Harkokin Mulki na kasa da  Malam Mas’udu Ibrahim Tulu, Mataimakinsa.
Da yake zantawa da wakilinmu kan nade-naden, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana godiyarsa  ga shugabannin kungiyar, kan irin hadin kan da Allah Ya ba su a cikin kungiyar.
Ya ce “Mun kusan kwana muna taro kan wannan magana a garin na Tambuwal, amma babu wani cece- ku-ce ko wata damuwa kan wannan zabe da muka yi. Don haka mun yi wa Allah godiya kan wannan nasara da ya ba mu, kuma muna sanar da duniya cewa wadannan su ne shugabanninmu na kungiyar Izala.”
Sheikh Jingir ya ce marigayi shugaban gudanarwar Alhaji Abdurhaman Marafa Tambuwal ya yi wa Musulunci aiki a tsawon rayuwarsa, don haka ya yi addu’ar Allah Ya jikansa Ya gafarta masa zunubbansa.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su rungumi harkokin ilimi da aiki da shi.  Ya ce, “Mu guji barin ’ya’yanmu suna zama kara-zube, yin haka shi ne yake sa batagari suke dibarsu suna jefa su a cikin ayyukan rashin da’a. Kuma mu zamanto masu biyayya ga shugabanninmu.”
Sabon Shugaban Gudanarwar, Sheikh Abdun-Nasir Abdul-Muhyi ya ca wannan nauyi da aka dora masa ya nuna cewa lokacin da yake da shi a rayuwarsa ya fara karewa, domin duk shugabannin kungiyar da aka yi guda biyar da suka rike wannan matsayi a yau ba sa raye. Ya ce don haka yake ganin wannan abu yana da nauyi kuma yana da ban tsoro.
Ya yi kira ga shugabanni su rika tausayawa na kasa, su kuma wadanda suke kasa su yi biyayya ga shugabanni. “Idan muka yi haka za mu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan,” inji shi.