Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya zama sabon Shugaban Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a ranar Asabar.
Sabon shugaban mai shekara 61 a duniya, zai kasance shugaban kasar na uku, a matsayin magajin Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, wanda ya rasu ranar Juma’a 13 ga watan Mayu, yana da shekara 73 a duniya.
- Taliban ta wajabta wa mata sanya nikabi a Afghanistan
- Yawan Amurkawan da ke neman ‘tallafin zaman kashe wando’ ya karu sosai
Sheikh Mohamed, wanda ya kasance Yarima Mai Jiran Gado na UAE daga watan Nuwamba 2004, yanzu shi ne zai zama Sarkin na 17 a jerin sarakunan Abu Dhabi, babban birnin kasar UEA.
Majalisar koli ta tarayyar kasar ta gudanar da zamanta a ranar Asabar domin zaben shugaban kasa, wanda zai yi mulki na tsawon shekara biyar, kafin ya samu damar sake tsayawa takara.
An zabo sabon shugaban ne daga cikin mambobin Majalisar Kolin tarayyar kasar.
Kazalika, Sheikh Mohamed, ya kasance Mataimakin Babban Kwamandan Sojojin Hadaddiyar Daular Larabawa, tun daga watan Janairun 2005.
Ya shahara wajen taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa rundunar tsaron UAE, ta fuskar tsare-tsare, horarwa, da kuma inganta harkokin tsaro.
A karkashin jagorancinsa, rundunar sojin UAE ta yi suna a matsayin babbar cibiyar da rundunonin sojin kasa da kasa ke yaba wa sosai.
UAE ta ayyana zaman makoki na kwan 40 daga ranar Juma’a bayan rasuwar Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, wanda ya fara mulkin tun a 2004.
Kazalika an rufe ofisoshin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu na tsawon kwana uku daga ranar Asabar, inda za a dawo aiki a ranar Talata 17 ga watan Mayu.