Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya nuna juyayinsa kan yadda masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da ’yan agajin kungiyar su 20, a karshen makon jiya.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya nuna juyayin nasa ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos. Ya ce ya shiga damuwa kwarai da gaske kan wannan abu da ya faru. “Domin ’yan agajin nan da dare da rana suna aikin taimakon jama’a ne, ba tare da ana biyansu albashi ba. Amma wani ya rike su ya ce su ba shi kudi, wannan akwai daukar alhaki kuma akwai rashin tausayi,” inji shi.
Ya ce don haka yana rokon masu garkuwa da mutanen su ji tsoron Allah su sako ’yan agajin da suka yi garkuwa da su.
“Abin da ya same ni shi ne a ranar Lahadi 23 ga Disamban da ya gabata, an kama mini ’yan agaji mutum 20, a yayin da suke dawowa daga wajen taron atisaye da aka gudanar a Jigawa. Suna hanyar komawa Sakkwato, sun shiga yankin Jibiya da ke Jihar Katsina, za su shiga Jihar Zamfara sai suka hadu da wadannan mutane suka tsayar da su, suka fito da su daga mota, suka tafi da su cikin daji suka bar motar a wajen. Don haka ina cikin matsala kan kama wadannan ’yan agaji, amma muna nan muna ta yin addu’a,” inji shi.
Sheikh Jingir ya jajanta wa iyalan ’yan agajin kan faruwar wannan lamari, kuma ya yaba wa kungiyoyin ’yan agaji na Fitiyanu da ’yan Darikun Kadiriyya da Tijjaniya da sauran kungiyoyin addinin Musulunci daban-daban, kan yadda suke ta yi masa jaje game da wannan lamari.
Sai ya yi kira ga gwamnatoci da malaman addini da sauran shugabannin al’umma a taru a bai wa tsaro muhimmanci, domin tsaro na kowa da kowa ne. Har’ila yau ya yi kira ga gwamnati ta samar da kayayyakin tsaro na zamani ta baiwa sojoji da sauran jami’an tsaron kasar nan. Kuma ta hada kai da kasashen da suke makotaka da Najeriya domin a magance matsalar tsaro da ake fama da shi.