Fitaccen malami a Kano, Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara ya maka Gwamnatin Jihar a gaban a Kotu, saboda hana shi wa’azi da kuma rufe majalisinsa da ke masallacinsa a Jihar.
Abduljabbar na neman kotun ta tabbatar masa na hakkinsa tare da hana gwamnatin da kuma ’yan sanda ci gaba da rufe masallacin nasa da kuma hana shi yin wa’azi.
- Wani hafsan dan sanda ya bindige kansa
- Bidiyon tsiraici: Dan hadimin Tambuwal ya gurfana a kotu
- Dubun masu kwacen waya a Kano ta cika
- An kama mijin malama yana mata satar jarabawa
Bayan sauraron karar a ranar Laraba, Kotun wadda Mai Shari’a Lewis Allagoa ke jagoranta ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis 18 ga Fabrairu, 2021.
Kotun ta kuma ba da umarnin mika sammaci ga Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda, wadanda su ne malamin ya shigar kara.
A makon jiya ne Gwamnatin Kano ta ba da uamarnin hana malamin yin wa’azi nan take saboda zargin sa da cin zarafin Sahabban Manzon Allah da kuma neman tayar da fitina a Jihar.
Ta kuma hana shin yin irin wadannan karatuttuka, ta hana kafafen yada labarai sawa a Jihar sannan ta rufe masallacinsa inda majalisinsa na As-habul Kahfi yake.
Abduljabbar na kalubalanta matakin ne da cewa tauye masa hakkin da doka ta ba shi ne na bayyana ra’ayi, walwala da gudanar da tarukan lumana.