Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya ce yana goyon bayan tubabbun ’yan kungiyar Boko Haram su dawo cikin al’umma, muddin hakan zai kawo zama lafiya.
Shehun Borno ya bayyana haka ne a taron kaddamar da shirin wayar da kai game da yin sasanci da kuma dawo da tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba da iyalansu cikin jama’a, wanday ya gudana Maiduguri.
- A bude wa ’yan bindiga wuta ko sun shiga cikin mutane —Masari
- ’Yan bindiga daga Zamfara da Katsina sun fara kai hari Kano
“Matsalar Boko Haram ba bakonmu ba ne, mun dade tana addabar mu, saboda haka idan har abun zai kare yanzu to muna muraba da hakan.
“Daga ni har hakimaina da dagatai da shugabannin addini da malamai duk mun yi amannar cewa sasasnci abu ne mai kyau a gare mu,” inji shi.
Basaraken ya kuma yi kira ga hukumomi da su yi aiki tare da kananan hukumomi da hakimai da dagattai a masu unguwanni a aikin samar da zaman lafiya.
A cewarsa, mastalar ta’addanci ta dauki shekaru tana gurgunta al’amura a Jihar Borno, shi ya sa mutanen suka yi maraba da yin sasanci da kuma samar da zaman lafiya.
Shehun Borno ya ce tubabbun ’yan Boko Haram din sun gane kuskurensu, saboda haka ya yi kira a zauna lafiya.
“Ba za a samu cigaba ba sai da zaman lafiya, muna kuma godiya ga Gwamna Babagana Umara Zulum a kan abubuwan alheri da yake wa mutanen jihar,” inji Shehun Borno.
Kwamishinan Yada Labarai da Raya Al’adu na Jihar Borno, Babakura Abba Joto, ya ce zuwa yanzu tubabbun ’yan Boko Haram 6,000 tare da iyalansu ne aka dauki bayanansu, kuma a shirye suke su dawo yin rayuwa a cikin jama’a.
“Akwai kuma mutum 200 da aka tursasa musu aiki a gonin kungiyar,” inji shi.
Babban jami’in ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Maiduguri, Phuong T Nguyen ya ce “mutane da dama da rikicin ya ritsa da su sun makale a yankunan da Boko Haram ta mamaye ta kuma talista musu yi masa aikin karfi da girki da leken asiri da noma da kuma dakon makamai.
“Wasu kuma an yi musu auren dole da ’yan kungiyar da dai sauran abubuwa.”
Kwamishinan Harkokin Mata ta Jihar Borno, Zuwaira Gambo, ta ce yawancin matan da suka mika wuya ba su da hannu a ayyukan Boko Haram; tilasta musu aka yi zuwa sansanonin kungiyar.
A don haka ta bukaci gwamnati ta ba su tallafi ta yadda za su koma cikin al’umma su ci gaba da rayuwa.