✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawarwari ga ma’aurata

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A yau in sha Allah za mu sanya sakonnin shawarwarin da masu…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A yau in sha Allah za mu sanya sakonnin shawarwarin da masu karatu suka aiko don gyara da inganta rayuwar aurensu. Da fatan Allah Ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
1.    Ina son in mika shawarata ga matan aure a kan su rika kiyaye kalmar lafazin da ke fitowa daga bakinsu; su rika la’akari da alfanu ko rashin su ga mazajensu.
—Ali Gusau  Mai-Doya  a garin Fatakwal
2.    Duniyar  ma’aurata  a gaskiya  na ji  dadin  bayaninku  na  wannan  makon a kan rashin kishin matanmu da ba ma yi. A gaskiya  mun bar  koyarwar  da  Annabi SAW Ya yi mana; mun bar  matanmu  suna  fita  irin  fita ta jahiliyya; mun sakar wa  matanmu  linzami  alhali  Allah SWT Ya ce  “ku kiyaye  kanku  da  na  iyalanku  daga  shiga wuta.”  Sai  ka ga  matan  Musulmi  sun hau babur  su  2 sun manne a jikin mai babur din. Da fatan Allah Ya sa mu dinga  kiyayewa ko ma samu dacewa da rahamar  Ubangiji, amin.
—Danlami  ibrahim  Mai Saida  jaridun  hausa.
3.    Shawara ga namiji mai neman aure: Yana da kyau wanda zai yi aure ya lura cewa ya kamata ya dara matarsa a abubuwan nan Uku: ilimi; hankali da kuma hakuri, sannan ya kasance sun yi tarayya a cikin abubuwa uku: Addini; fahimtar juna da kuma hakuri, sannan ana son ya kasance ita ta dara shi da abubuwa uku: Kwalliya; iya girki da kuma biyayya.Wannan zai taimaka wajen zaman aure ya dore, kuma da zarar matsala ta faru nan da nan za a fahimci juna.
—Muhd A. Sani Kano.
4.    Idan amarya za ta shigo gidan mai mata ya kamata ta lura da kyau kuma ta yi hakuri; domin su maza akwai su da tsananta doki, don haka kada ta dauka wannan dokin zai dore, domin in ta yi haka, bayan dokin ya wuce sai ta samu matsala.
5.    Ina karuwa matuka da karanta Aminiya ta hanyoyi da dama, yanzu abin da ya rage shi ne, ku kirkiro mana filin hada zumuntar auratayya; kun ga ke nan ga filin hada mata da maza aure kuma ga filin koya musu yadda za suyi zaman lafiya. Nagode, da fatan sakona zai sami shiga.
—I B A Gombe
6.    A gaskiya namiji ba dan goyo ba ne! Wallahi in har mace ba ta shiga ransa ba, to ba za ta taba yi masa gwaninta ba! Komai ta yi masa maimakon ya yaba mata to sai dai ya kara ma bata mata rai.
7.    A gaskiya wasu matan su ne ba su yin adalci ga mazajensu, saboda komai kake yi wa mace sai ta raina ma hanzari ko ta bata maka rai, ka ce ba ka son abu, amma sai makwabta da abokai su janye mata hankali ta ki maganarka. Kuma mai ya sa wasu matan ke kiran mazan da ba muharaminsu ba a waya a boye? Kuma ko da biki ya kama ka hana ta zuwa sai ta kama fushi da kai. Wajen kwanciya ta ce ma wai ita ba ta san dadin wannan ba ko da shekara za ta yi ba a kusance ta ba ba ta damuwa.
—Bashir Zamfara
8.    Ina son in ja hankali masu nema ko karin aure, musamman wadanda Allah Ya jarraba da wata cuta da su rika neman shawarar likita game da dacewarsu domin saukaka zamantakewarsu (a su kansu da ‘ya’yan da za su haifa). Abin da ya jawo na yi wannan kira shi ne: Wani ya tambayi likita a filin kiwon lafiya, yake bayanin yadda ‘yarsa take fama da cututtuka sakamakon sikila da take da shi. Tambayar farko da likita ya yi masa ita ce, me ya hana su neman shawara tun kafin su yi aure tun da shi da matar duk suna da sikila? Hakan zai iya jefa su kullum cikin wahalar neman lafiya ga ‘ya’yan da suka haifa, ban da sukurkucewa da zamantakewarsu ka iya samu.
—Muhammad S Abubakar T/murtala Kano
9.    Don Allah ina so in ja hankalin mata masu satar kayan abincin da mazajensu ke sayowa don amfaninsu, amma sai matan su dinga sayarwa ko kuma su dinga raba wa kawayensu da ‘yan uwansu kyauta. Wannan haramun ne kuma mummunar dabi’a ce; Allah Ya shirye mu, amin.
—Muhammad Ashiru Abayo ‘Yankaba.
10    Ina son in yi nasiha ga matan da suke aure saboda abin duniya, har su bari ana saduwa da su ta dubura kuma su ci gaba da zama da mazan a haka, saboda abin duniya. Su ji tsoron Allah su tuba ko sa dace da rahamar Allah ranar gobe kiyama.
—Magatakardan Hakimin Pambegua.

1.    Ni ba matashi ba ne, amma ni’imar da Allah ke wa bayinsa ta aure har yanzu bai yi mini ba, dalili ke nan da nake fama da wannan masifa ta zinar hannu don guje wa zina, ba don ina so ba nake yi, Wallahi. Yanzu na dada firgita da gigita da na ji illarta, kuma na tuba in sha Allah, ina rokon Allah Ya taimaka ya sahale min rabuwa da wannan bala’i; don girman Allah ‘yan uwa ku taya ni da addu’a.
—Ibrahim.
2.    Ina kira ga matan Hausawa su dinga yin kokari wajen biya wa mazajensu bukatar aure, domin ni dai biyan bukatata da hannuna ya fi min sauki a kan in tunkari maidakina
—Abubakar Kaduna