Assalamu alaikum jama’a, da fatan muna lafiya. Da farko dai na kasance babban masoyin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda tun a lokacin da muke yara yake takarar Shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar ANPP mai masara ina son sa, so na hakika, ina yi masa addu’o’in fatan alheri tare da samun nasarar cin zabe ba dare ba rana, aka zo bai samu nasarar cin zaben ba. Aka sake dawowa a shekara ta 2011 a karkashin jam’iyyar CPC mai alkalami, ya kara yin takara amma bai samu nasarar cin zabe ba kuma amma a wancan lokacin talakawa na tare da shi kuma suna goyon bayansa. Uwa uba guguwar canji ta kada a shekara ta 2015 inda ’yan Najeriya suka hada kawunansu waje daya tare da cire bambance- bambancen da ke tsakaninsu kama daga na addini da na kabilanci da dai sauransu, domin ganin sun cimma nasarar sauya Shugaba Goodluck Ebele Jonathan. Na kasance daya daga cikin wadanda suka yi azumi tare da bayyana jin dadi mara adadi da godiya ga Allah a kan ba Shugaba Buhari nasara, kai duk wani abin da dan kasa zai yi wajen bayyana jin dadinsa da farin ciki a kan cin zaben Shugaba Buhari na yi.
To amma sai na fahimci wasu abubuwa da gwamnatin Baba Buhari take yi wadanda ba su yi wa talaka irina dadi ba. Wadannan abubuwa sun hada da hauhawar kayan masarufi, ma’ana tashin gwauron zabin da kayayyakin suka yi wanda hakan ya biyo bayan durkushewar tattalin arzikin Najeriya. An yi ta kokarin a ga an bullo da hanyoyin da za a habaka tattalin arzikin don talaka ya samu sa’ida amma abin ya ci tura.
A bangaren tsaro Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokari, musamman a bangaren yaki da ’yan Boko Haram, sai dai a bangaren fadace-fadacen kabilanci da na satar mutane ko yin garkuwa da su ana karbar kudin fansa, kullum abin sai gaba yake kara yi, ka ga a nan ya kamata Buhari ya yi wani abu a kai.
Baya ga wadannan, akwai matsaloli da dama da gwamnatinsa ta jefa talaka a cikin kunci da suka hada da karin kudin fetur da rashin wadatarsa da matsalar daukewar wutar lantarki da na rashin kyawun hanyoyi a fadin kasar nan da matsalar rashin ayyukan yi ga dimbin matasanmu da hakan ta sa suka shiga shaye-shaye da sauran miyagun ayyuka.
A kan haka nake ba Shugaba Baba Buhari shawara da kada ya ce zai sake tsayawa takara a karo na biyu a shekarar 2019 domin yanzu Najeriya tana bukatar matashi ne mai jini a jika, haziki wanda zai iya fitar da mu daga wannan kangi da muka tsinci kanmu a ciki.
Soyayyar da ke tsakanina da kai Baba Buhari ba za ta hana ni fada maka gaskiya ba, ko ba ka shawara a kan abin da na ga ya dace.
Allah Ya zaba mana duk abin da ya fi zama alheri ga kasarmu Najeriya.
Nura Sani Rijau, dan gwagwarmaya mai kare hakkin dan Adam. Za a iya samunsa a lambobi kamar haka: 08108291641 08026664213