✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawara ga Shugaba Buhari da manyan Arewa maso Yamma 

Da farko zan fara da Shugaba Muhammadu Buhari da tsatsonsa yake wannan yankin da yake da mafi yawan al’ummar Najeriya da jihohi mafiya yawa guda…

Da farko zan fara da Shugaba Muhammadu Buhari da tsatsonsa yake wannan yankin da yake da mafi yawan al’ummar Najeriya da jihohi mafiya yawa guda bakwai.

Mai girma Shugaban Kasa, zan ɗan yi maka wani tuni. Kai ne mutum ɗaya tal a tarihin dimokuradiyyar Najeriya da ya ci zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar adawa tare da kayar da Shugaban Kasa mai ci, ba kuma tare da an sayi al’umma da kuɗi ba. A tarihin Najeriya ba a taɓa yin ko kusa ga haka ba. Kuma tsantsar ƙaunarka da mu talakawan Najeriya ke yi ne ya sa muka zaɓe ka, saboda aminci da yarda da muke da su a kanka bisa tunanin za ka iya tsamo ƙasarmu daga taɓon da ta faɗa har ya hana ta yin gaba. Hakan ya sa duk kuɗin da gwamnatin da ka kayar ta bayar do ta zarce a mulki bai yi tasiri wajen  hana kawar da ita daga kan mulki ba.

Babban abin da ya sa muka ki gwamnatin Goodluck Jonathan a lokacin muka jefar da shi kwandon shara bai wuce matsalar rashin tsaro da ta addabi Arewa maso Gabas da mafi yawan jihohin Arewa ba, inda a lokacin Boko Haram ta yi wa mummunar barna. Sakacin gwamnatin ya sa kullum ’yan Boko Haram suna cin karensu babu babbaka tare da ƙara faɗaɗa ayyukansu na ta’addanci a ƙasa.

Alhamdulillahi mun zaɓe ka kuma ka yi ƙoƙarin cin galabar Boko Haram da kaso mai girma. Domin an ci nasara a kansu matuƙar gaske, tare da ƙwace dukkan ƙananan hukumomin da suke iko da su a baya. Tare da tsayar da faɗaɗa aikin ta’addancinta. Tabbas mu al’ummar Arewa da Najeriya mun yaba da hakan, kuma muna ci gaba da alfahari da haka.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Mai girma Shugaban Kasa, a yau an wayi gari yankinka ya faɗa cikin irin wancan mummunan hali na matsalar tsaro. Da farko abin yana faruwa ne kurum a jihata ta Zamfara, wanda har yanzu nan ya fi muni. Mu mazauna Zamfara mun san akwai sakaci ɗari-bisa-ɗari na gwamnanmu a kan ci gaba da kashe-kashen da ake yi mana. A baya matsalar ko a Jihar Zamfara da abin bai wuce wasu yankuna na Maru da Ɗansadau da ’Yargaladima da ƙauyen Kizara a Karamar Hukumar Tsafe ba, sannu-sannu abin ya faɗaɗa, har aka wayi gari mummunan rashin tsaron ya mamaye Zamfara baki ɗaya kullum cikin zubar da jini ake yi.

Ran dan Adam ya zama kamar na kiyashi, fyaɗe da satar mutane da ƙone dukiyar jama’a sun zama ƙawa a jihar baki ɗaya. Sannu-sannu ya shiga maƙwabtan jihohin Sakkwato da jiharka ta Katsina da garinka Daura a makon jiya, inda aka sace surukin dogarinka. Haka zalika in muka duba sannu-sannu matsalar ta karaɗe kusan dukkan jihohin yankin bakwai. Kuma kullum matsalar ƙaruwa take yi musamman a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sakkwato da Neja da kuma Jigawa, Kano kaɗai ce abin ke da dama-dama, kuma ko ita abin ya yi masifar taɓa ta, domin hanyar zuwa jihar ta zama tarkon mutuwa ga Zamfarawa da Katsinawa da Sakkwatawa da Kabawa.

Mai girma Shugaban Kasa, kaɗan ke nan daga cikin matsalar tsaron da ke fuskantar yankinka. Haƙiƙa wannan yanki na buƙatar gudunmawarka ɗari-bisa-dari,  domin har yanzu ainihin matsalar tsaro a yankin ba a ɗauko hanyar magance ta yadda ta dace ba. Domin jami’an tsaro da ke iya tsayar da matsalar sun ƙaranta da kayan aikinsu matuƙar gaske, inda ko a ranar 5-5-2019 Sarkin Kudun Ɗansadau ya shaida wa duniya a shirin safe da hantsi na BBC Hausa cewa kashi 60 cikin 100 na matsalar tsaro a Zamfara a Masarautar Ɗansadau yake amma har yanzu ba a kawo musu jami’an tsaron da za su fuskanci matsalar ba.

Haka zalika akwai wasu matakai da aka ɗauka wanda alhamdulillahi ɗayan zai taimaka matuƙar gaske. Wato hana haƙar ma’adanai a Jihar Zamfara ta nan ne cibiyar tashin hankalin Arewa baki ɗaya, to amma wallahi matakin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauka na taƙaita yawo da babura a wani lokaci wanda yanzu har ya kai an haɗa da babura masu ƙafa uku (Keke NAPEP) haƙiƙa wannan mataki yana taimakawa ne kurrum wajen ƙara janyo masifa ga al’ummar jihar. Domin masifaffen rashin aikin yi ya ƙaru. Ga masu neman abinci da babura tare da jefa al’ummar da ba su ji ba su gani ba cikin masifa. Kwatsam na ji a Sashin Hausa na BBC, cewa an haramta yawo da babura a wasu jihohin yankin.

Mai girma Shugaban Kasa, bala’in da mu al’ummarka muke ciki wallahi yana buƙatarka kacokan! Kuma wallahi muddin ka yi sake sai wannan matsalar ta zarce ta Boko Haram a Najeriya.

Dole a ɗauki matakan sama wa matasa makoma tagari ba wai kara jefa su cikin masifu da ake yi yanzu ba.

Haka zalika ku kanku jagororin wannan yankin wallahi kuna da babban aiki a gabanku. Domin kun yi shiru ana kisan al’ummarku duk wata gudunmawa da za ku iya bayarwa kun ƙi a zahirance. Ƙila kuna taƙamar kuna da dukiyar da za ku iya ɗaukar hayar jirgi ya kwashe muku shirginku ko? Idan haka ne to, kun yi ragon tunani, domin ba ku da inda ya fi muku wannan yanki, nan Allah Ya halicce ku, nan za ku zauna ku ji daɗi kowace duniya kuka je za ku buƙaci dawowa gida cikin al’ummarku.

Don haka ya zama dole ku kanku ku tashi tsaye ku bayar da taku gudunmawa tun daga ta taimakawa a yaƙi talauci da rashin aikin yi da ya yi wa yankinku katutu har ya taimaka wajen samuwar ƙungiyoyin ta’addanci, kuma ku taimaka da shawarwari da matsin lamba ga Shugaba Buhari ya kalli al’ummarsa, kamar yadda na wasu yankuna ke yi.

Ina ganin yanzu akwai buƙatar yin wata ma’aikata da za ta kula da farfaɗo da yankin Arewa maso Yamma kamar yadda ake da ta Neja-Delta da Arewa maso Gabas. Domin ta kula da na farko dai abin ya kawo tada zaune-tsaye a wannan yanki da hanyoyin da suka  dace a bi domin magance matsalolin da kuma ƙoƙarin sake fasali da ƙara gina yankin baki ɗaya. Domin ni dai wallahi na san yanzu kashi 40 cikin 100 na mutanen Zamfara sun tarwatse musamman na karkara da ake kisa kullum.

Muddin aka yi haka to da ikon Allah zaman lafiya zai samu a yankinmu, kuma ci gaba zai zo insha Allahu.

A ƙarshe muna rokon Allah Ya ɗaukaki wannan yanki namu da Arewa da ƙasarmu Najeriya. Ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa, Ya ba mu shugabanni nagari.

Muna roƙon Allah Ya sa wannan koke namu ya kai ga waɗanda muka yi dominsu Ya kuma ba su ikon share mana hawayenmu. Allahumma amin.

Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu, Gusau, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara, 08069807496