Yau Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022 kotun Musulunci da ke Kano za ta yanke hukunci a Shari’ar zargin yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke fuskanta.
A makon jiya ne Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano ta sanar da ranar ranar yanku ewa Sheikh Abduljabbar hukunci ta bakin Kakakin Manyan Kounan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Muzammil Ado Fagge.
- Yau saura kwana 47 cif a daina karbar tsoffin kudade
- Kotun Kano ta yanke wa dan Hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya
A watan Yuli na shekarar 2021 ne Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abduljabbar a gaban kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, bisa zargin malamin da yin batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma tayar da hankalin jama’a.
Shari’ar dai ta dauki hankali tun wancan lokaci, kafin wannan lokaci da aka tsayar da ranar yanke hukuncin da kotun za ta yi wa fitaccen malamin.