✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shan Shisha zai iya haifar da ciwon zuciya —Bincike

Binciken ya gano akwai alaka tsakanin cutar da shan Shisha

Wasu masu bincike a Jami’ar Kasar Qatar a kwanan nan sun gano cewa masu shan hayakin Shisha na cikin barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Shisha dai wani hayaki ne mai dauke da fulebo da ake shaka ta cikin wani bututu, wanda ya samo asali daga kasashen Gabas ta Tsakiya.

Wani Farfesa a Sashen Koyar da Likitanci na jami’ar ta Qatar, Susu Zughaier, ne ya jagoranci gudanar da binciken.

Binciken dai ya yi nazarin alkaluma ne daga sama da mutum 1,000 da ke zaune a kasar ta Qatar, kamar yadda wata sanarwa da jami’ar ta fitar ranar Alhamis ta bayyana.

Masanan dai sun gano cewa masu shan Shishar sun fi barazanar kamuwa da ciwon da sama da kaso 1.65, idan aka kwatanta su da wadanda ba sa sha.

Kazalika, fara shan Shisha tun da kuruciya na da matukar alaka da barazanar kamuwa da cutar bayan an girma.

Binciken dai ya ba da gagarumar gudunmawa wajen fahimtar illolin da shan Shishar ke da shi, inda ya nuna akwai bukatar sake duba barazanar ab kasar da ma a wasu kasashen. (Xinhua/NAN)