Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta bukaci a kafa sabbin dokoki masu tsauri domin hukunta masu safara da masu shan miyagun kwayoyi domin yakar manyan laifuka.
Shugaban NDLEA, Muhammad Marwa, ya bayyana hakan ne a Abuja, ranar Laraba, a taron kasa karo na biyar kan shaye-shayen kwayoyi a Najeriya, wanda cibiyar bincike da samar da bayanai kan cin zarafin al’umma ta shirya.
- Wani saurayi dan acaba ya mayar da N20m da ya tsinta
- Gwamnati ta yi gwanjon rigar nonon Diezani a kan $12.3
A cewarsa, tarar da aka ci ba ta da tsaurin da za ta hana masu aikata laifukan ta’ammali da muggan kwayoyi.
Ya ce yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a bana yana samun gagarumar nasara domin ana kama masu aikata laifuka da dama.
Ya ce hukumar ta NDLEA ta tuntubi gwamnatocin jahohi su dauki yakin zuwa lunguna da sako a fadin jihohinsu.