✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaikh Dahiru Bauchi ya ja layi da gwamnoni kan almajirci

Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya Shaik Dahiru Bauchi da malaman makarantun allo sun yi barazanar daukar mataki kan gwamnonin da suka hana almajirci a jihohinsu.…

Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya Shaik Dahiru Bauchi da malaman makarantun allo sun yi barazanar daukar mataki kan gwamnonin da suka hana almajirci a jihohinsu.

Martanin malaman ga dokar hana karatun almajirci da gwamnonin suka yi, ya ce za su kayar da gwamnonin a zabe kuma almajirai na da ‘yancin yin addini da neman ilimi a duk inda suke so a Najeriya.

“Almajirai da alarammomi na da ‘yancinsu a matsayin ‘yan Najeriya su yi addini, su kuma zauna a inda suke so kuma ba za mu lamunci duk salon tauye mana hakki da sunan dokar hana almajirci ba, ana dibar almajirai daga wata jiha zuwa wata kamar dabbobi”, inji Shaikh Dahiru.

Sanarwar tasu na zuwa ne bayan gwamnonin Arewacin Najeriya sun haramta tsarin karantun da kuma bara, tare da mayar da almajiran gaban iyayensu domin dakile yaduwar cutar coronavirus da kuma hana barace-barace.

Da yake jawabi a taron alarammomin kan dokar, Shaikh Dahiru Bauchi ya ce, “Dole mu zauna tare da almajiranmu mu koya mu kuma koma musu Alkur’ani da haddarsa kamar yadda aka gada sama da shekara 1,000; Ba mu bukatar wani ya ce zai sauya mana al’adar karatun Alku’ani”.

 

Gwamnati ta kasa magance talaucin da ke sa bara

Game da yawon barace-baracen almajirai kuwa, cewa ya yi, “Shin almajirai sun je rokon abinci gidajen gwamnonin Arewan ne? A gidajen al’umma a yankunan da suke zama suke barar abinci kuma jama’a ba su gaji da mu ba.

A makalarsa kan hakkokin almajirai a doka ga taron, Barista Aminu Balarabe Isa ya ce haramta karatun almajirci saba dokar kasa ne da ta ba da‘yancin neman ilimi.

Taron da aka gabatar da makaloli shida a cikinsa ya bayyana talauci a matsayin ummul-haba’isin barace-barace a Najeriya, wanda suka ce gwamnati ta kasa magancewa.

A cewarsu, shi ya sa bayan rufe makarantun allon ma ake ci gaba da barace-barace a tituna da ofisoshinn gwamnatin kuma ta kasa hana su.