Aminiya ta tattauna da Alhaji Buba Galadima, daya daga cikin mutum tara da suka sanya hannu aka haifi Jam’iyyar APC, domin jin ta bakinsa game da ficewar Shekarau da Bafarawa daga Jam’iyyar APC, kamar haka:
Aminiya: Tun ba a yi nisa ba, sai ga shi jam’iyyarku ta APC ta fara fuskantar rigingimu. Na baya-bayan nan shi ne ficewar tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Sakkwato, Malam Ibrahim Shekarau da Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa zuwa Jam’iyyar PDP. Yaya kuka ji da wannan lamari?
Buba Galadima: Maganar gaskiya, ficewar wadannan muhimman mutane biyu, kai ko da wadanda ba su kai su ba ne ma, babbar asara ce ga jam’iyya, saboda kuri’ar mutum daya kawai na iya sanadin nasarar dan takara. Saboda haka ni, a kashin kaina, na ji zafin fitarsu, saboda suna da iyali da abokan hulda da kuma mabiya.
Aminiya: Sun yi ta korafi, gabanin ficewarsu, cewa ba a yi musu adalci ba, sai dai ba a samu nasarar sasanta matsalar ba har suka fice, me kake jin ya kai ga hakan?
Buba Galadima: Da farko dai zan ce samu ya fi iyawa, hawan dokin maciji, domin da ina da iko a shugabancin jam’iyyar nan da na yi wani abu sabanin abin da ake yi a yanzu. Saboda a baya ba mu wuce mu uku ba a lokacin da muka fara zawarcin gwamnonin nan da sauran manya ire-irensu zuwa wannan jam’iyyar, kafin jam’iyya ta karbi al’amarin daga hanunmu. Kodayake ba lallai ba ne mu san duk wani abin da ya kai ga wannan sabani a tsakaninsu da jam’iyya. Wani abu da ke zahiri shi ne, jam’iyya ta yi kuskure wajen zuwa jihohin Sakkwato da Kano a yayin zawarcin gwamnoninsu ba tare da sanar da jagororin jihohin ba da al’ummarsu. Kamata ya yi a ce sun sanar da shugabannin jam’iyyu ukun nan da suka hadu suka yi wannan hadaka, ko akalla su gana da su a lokacin da suka je jihohin gabanin ganawarsu da gwamnonin ko bayan sun gana din, ko ma su yi musu tayin kai ziyarar tare da su, wato ina nufin irin su Bafarawa da Shekarau. Idan sun amsa gayyatar falillahil hamdu, idan ko ba su je ba, to ba su da dalilin yin korafi, watakila da ba a samu irin wannan rashin jituwar da ta biyo rashin sanar da su da aka yi ba. Wannan ina ganin shi ne kuskuren da shugabannin jam’iyyarmu suka yi.
A gefe guda kuma su masu wannan korafi idan don al’ummarsu da kasarsu suke yin wannan gwagwarmayar, ba don kansu ba, ban ga abin da zai taba imaninsu har ya kai su ga komawa waccan jam’iyya ba. Tun ma ba Malam Ibrahim Shekarau ba, saboda al’amarinsa ya bambanta da na Bafarawa, wanda rashin adalcin da aka yi masa, yana da girma. Kuma ina ganin jin dadi ne ya yi wa Shekarau yawa har yake cewa ba a yi masa adalci ba. Ya tuna fa a shekarar 2003 lokacin da ya shigo Jam’iyyar ANPP, a cikin wata biyu aka dauki kujerar takarar Gwamna aka ba shi, bayan tun farko wanda ya raine ta na tsawon shekara hudu, wato Malam Ibrahim Al’amin Litil ya samu nasarar kayar da shi a zaben fidda dan takara. Saboda kawai dogewa da wadansu suka yi na sai an ba shi kujerar a bisa dalilansu da su ne suka sani. Kuma ni din nan a kungiyarmu ta Buhari Organaizeshon bayan an tsara hakan, sai muka yi ruwa muka yi tsaki, inda Janar Buhari ya sa hannu aka saki kudi daga kungiyar aka yi aikin zabe. Amma a karshe bayan Malam Shekarau ya zama Gwamna, sai da ta kai ba ya ko gaisuwa ta Musulunci da ta zama dole tsakaninsa da mutum takwas da suka taimaka masa Allah Ya ba shi nasara. Kai karewa ma, hatta Janar Buhari kowa ya ji irin bayanan da ya yi a kansa a rediyon Muryar Amurka, sannan a karshe wadansu suka zuga shi har ya kai ga yin takara a tsakaninsa da shi a zaben 2011. Idan ko ana zancen girma ne ya sa yanzu ya bar APC zuwa PDP, ai Kabiru Gaya ya grime su dukansu, shi da Kwankwaso, don ya yi Gwamnan Jihar Kano gabanin su yi, amma ana tare da shi bai yi korafin an ci zarafinsa ba. Idan ko a tsakaninsa da Kwankwaso ne, ai ya san ba ya hada kansa da shi, saboda Kwankwason nan ya riki Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, ya yi Jakada, ya yi Ministan Tsaro na shekara hudu, ya yi Gwamna a lokacin da shi Shekarau ke matsayin Babban Sakatare a gidan gwamnati a lokacin da Kwankwaso yake Gwamna, wanda cikin ayyukansa har da tattara fayil sannan ya kawo masa ya sa hannu. To fisabilillahi da wannan ne har za ka tsaya kana jayayya da shugabancinsa a kanka, alhali shi ne Gwamna a jihar? Kuma tsarin shugabantar da shi da kai ne aka tsara a jam’iyyance. Idan ka duba wannan duka, kai ka san son kai ne ya sa Malam Ibrahim Shekarau ya jajirce a kan wannan jayayyar, amma ba don rashin gane gaskiya ba.
Aminiya: A baya kai ne Sakataren CPC, amma a wannan tafiyar ba ka rike da komai, me ya bambantaka da shi da kai ba ka fice daga wannan tafiyar ba?
Buba Galadima: Ni ba na neman takarar dan Majalisar Tarayya ko Gwamna ko Shugaban kasa, babbar damuwata ita ce koma-baya da yankina da al’ummata da kasata ke fuskanta, sai kuma yin duk abin da ya dace don kawo karshen wannan kashe- kashe da cin mutunci da ake yi wa yankina.
Aminiya: Bayan rinjaye da jam’iyyarku ta samu a Majalisar Wakilai sai ga shi wasu ’yan majalisa na sauya sheka zuwa PDP, ta wace hanya kake jin za a magance wannan matsalar?
Buba Galadima: Ina ganin shugabanninmu sun yi rauni a yadda suke tafiyar da jam’iyyar bayan gagarumin rinjaye da muka samu a majalisar bayan shigowar sababbin gwamnonin nan zuwa jam’yyarmu. Dole ne su riki ’yan majalisa da muhimmanci, sannan su sadaukar da duk abin da zai taimaka wajen shawo kansu ta hanyar yi musu alkawura nagari tun da dai ba mu da dukiyar mai irin wadda yanzu ake amfani da ita ana raunana zukatan wasu ’yan majalisar, inda ake zargin ana saye su da Dala miliyan guda na Amurka da kuma abin da ya fi haka, karkashin kwamiti na musamman da PDP ta nada. wannan sabon salo ne sabanin na Bamanga Tukur da yake bude musu idanu.
Aminiya: To wane kokari kake ganin ya kamata a yi wajen sulhunta wasu shugabannin jam’iyyar da ke takaddama a halin yanzu, gabanin su ma su dauki mataki irin na Shekarau da Bafarawa?
Buba Galadima: A gaskiya wannan matsala ta fi karfi a yankinmu na Arewa, ban ji dadin yadda na ga matsalar takaddama ta kai Gwamnan Borno Kashim Shetima da tsohon Gwamna Ali Madu Sharif zuwa Legas ba, har ma shawo kansu a can din, aka ruwaito ya gagara, shin ba mu da dattawa ne a nan Arewa da ba za su iya sasanta su ba? Ko shi Bafarawa gabanin ficewarsa, kana jin zai ji dadin bude bakinsa ya yi ta fadin sirrin jiharsa ga Oyegun, idan da wani daga nan Arewa aka hada, sai ya sasanta su.
Shagwaba ce ta sa Shekarau ya ce ba a yi masa adalci ba – Buba Galadima
Aminiya ta tattauna da Alhaji Buba Galadima, daya daga cikin mutum tara da suka sanya hannu aka haifi Jam’iyyar APC, domin jin ta bakinsa game…
