✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaguna 13,000 gobara ta kone a kasuwar ‘Monday Market’ —Zulum

Gwamnan ya ce akalla mutum 20,000 ne gobarar ta shafa a jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar ‘Monday Market’ ta Maiduguri ta lalata shaguna 13,000.

Zulum ya shaida wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, cewa gobarar ta lalata dukiyar ’yan kasuwa akalla 20,000.

Ya shaida wa shugaban kasa cewa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta hannun Ma’aikatar Agaji da Jin Kai, ta bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.

“Bugu da kari, gwamnatin Borno ta bayar da tallafin na Naira biliyan daya don rage wahalar da mutanen da abin ya shafa ke fuskanta,” in ji Zulum.

Ya bayyana jin dadinsa kan ziyarar da Shugaba Buhari ya kai kan lamarin, ya kuma ce jama’a na sa ran samun goyon bayansa.

A nata jawabin, Ministar Harkokin Jin Kai, Sadiya Farouq, ta ce an bayar da tallafin ne ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa da kuma hukumar NEDC.

“Sun yi aiki kafada da kafada da gwamnatin Borno domin samun wasu kayayyaki, amma abin takaici, babu wani abu da aka tsira da shi a gobarar.

“Mun samar da buhunan shinkafa 30,000, buhunan masara 30,000 da kayan abinci da sauransu a matsayin tallafi.

“Na ba da umarnin ci gaba da tantance wadanda abun ya shafa kuma za mu bayar da karin tallafi da kayan gini,” in ji Farouq.

Ministar ta ba da tabbacin cewa za a mika rahoton tantancewar ga ofishin shugaban kasa domin shahalewa.

Shugaba Buhari, wanda ya kai gaisuwar ban girma ga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar-Garbai El-Kanemi, ya bayyana alhininsa da afkuwar lamarin.