Kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint Germain ta dauki Sergio Ramos a matsayin sabon dan wasanta.
Kungiyar ta PSG ta cimma yarjejeniyar shekara biyu da Ramos, zuwa karshen kakar wasanni ta 2023.
- EFCC na neman hadimin Tambuwal kan damfarar N2.2m
- Mun aika ‘yan ta’adda da yawa lahira —Hafsan Sojin Kasa
Tsohon kyaftin din na Real Madrid ya sauya shekar ne zuwa PSG bayan karewar kwantaraginsa da kungiyar a karshen watan Yuni, 2021.
Ramos ya shafe shekara 16 a Real Madrid kafin daga bisani ya raba gari da ita.
Dan wasan mai shekara 35 a duniya ya buga wa Madrid wasanni 671 sannan ya zura kwallaye 101, tare da lashe kofi 22 da kungiyar.