Dan wasan bayan Real Madrid, Sergio Ramos ya kamu da cutar COVID-19 kamar yadda kungiyar ta sanar a shafinta na intanet a ranar Talata.
Ramos mai shekaru 35 a duniya wanda shi ne Kyaftin din kungiyar, ya killace kansa kamar yadda ka’idodin mahukunta suka tanadar.
Ana sa ran Ramos zai dauki tsawon wata guda ba tare da taka leda a kungiyar ba, sakamakon raunin da yake fama da shi da kuma kamuwa da cutar Coronavirus da ya yi.
Ya zuwa yanzu dai ’yan wasan Real Madrid da suka kamu da cutar sun hada Rapahel Varane, Mariano Diaz, Eden Hazard, Eder Militao, Casemiro, Luka Jovic, Nacho Fernandez da kuma kocin kungiyar, Zinedine Zidane.
Lokaci na karshe da aka ga Sergio Ramos a filin wasa, shi ne ranar Asabar din da ta gabata a matsayin dan kallo, yayin wasan da Real Madrid ta yi nasara kan Barcelona da ci 2-1.
Zinedine Zidane, ya kafa tarihin zama kocin kungiyar na farko cikin shekaru 42 da ya jagoranci samun nasara kan babbar abokiyar hamayyarsu Barcelona sau uku a jere yayin wasannin El Clasico da suka fafata.