✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Senegal ta dakatar da qwallo sai bayan zave

A ranar Lahadin ta gabata ne gwamnatin Senegal ta bayar da sanarwar dakatar da gudanar da yin qwallo a kowane mataki a qasar har sai…

A ranar Lahadin ta gabata ne gwamnatin Senegal ta bayar da sanarwar dakatar da gudanar da yin qwallo a kowane mataki a qasar har sai bayan an kammala zavuvvukan da ke tafe a qasar wanda za a gudanar a qarshen wannan wata da muke ciki. Haka kuma qasar ta umarci a dakatar da duk waxansu tarurrukan da suka shafi na al’adu kamar na bukukuwan aure ko na suna ba tare da amincewar gwamnati ba.

Gwamnatin ta xauki wannan mataki ne bayan an samu asarar rayukan kimanin mutane takwas  a filin wasa na qasar a ranar Asabar da ta gabata bayan wata katanga ta faxa musu a lokacin da ake cikin tsakiyar wasa.  Hakan ta janyo kimanin mutane 61 suka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti.

A ranar 30 ga wannan da muke ciki ne ake sa ran za a gudanar da zaven shugaban qasar kuma kawo yanzu hankali ya fara tashi ganin yadda xaya daga cikin ’yan adawa Khalifa Sall yake samun magoya baya duk da yake yana gudanar da kamfen xin neman a zave shi ne daga kurkuku.

Mai magana da yawun Firaministan qasar Seydou Gueye ya ce “gwamnati ta dakar da gudanar da wasannin qwallo da tarurrukan da ba a amince da su ba a duk faxin qasar har sai an kammala zave”.  Ya ce an xauki wannan mataki ne don a kawar da fargabar tashin hankali.

An samu kimanin rasuwar mutum takwas ne bayan wata katanda da ke filin wasa na Dakar ta faxa a kansu yayin da mutum 61 kuma suka ji rauni kuma aka garzaya da su asibiti a ranar da aka yi wasan qarshe na cin kofin qalubale na qasar a tsakanin kulob xin Stade de Mbour da kuma na US Onakam al’amarin da ya kawo hargitsi a tsakanin magoya bayan qungiyoyin qwallon qafar biyu kuma aka dakatar da wasan, kamar yadda Ministan Wasanni na qasar Matar Ba ya faxawa kafar watsa labarai ta AFP.

Asarar rayukan ta sa Kwamitin yin kamfe na Shugaban Qasa Macky Sall ya dakatar da kamfen xin da yake yi a ranar Lahadin da ta gabata don yin jimami ga waxanda suka rasu da kuma waxanda suka samu rauni.

Rahotanni sun ce magoya bayan shugaban qasar da kuma na xaya daga cikin ’yan adawa sun yi ba-ta-kashi a ranar Juma’ar da ta wuce a lokacin da suke yaqin neman zave al’amarin da yake ci gaba da kawo zaman xar ganin tun kafin ranar zaven hankula sun fara tashi.