✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SEC ta haramta hadar-hadar ‘Binance’ a Najeriya

An gargadi masu mu’alama da kamfanin Binance da su dakata.

Hukumar Kula da Hada-Hadar Hannayen Jari ta Najeriya SEC ta haramta ayyukan kamfanin hada-hadar kudaden intanet na Binance a kasar.

Matakin na kunshe ne a cikin wata sanarwar ta hukumar ta SEC wato Securities and Exchange Commission ta wallafa a shafinta intanet.

SEC ta ce kamfanin na Binance bai yi rajista da ita ba, a don haka ne ta ce ta haramta ayyukan kamfanin a fadin kasar.

Sanarwar ta kuma gargadi ’yan kasar da ke mu’alama da kamfanin da su dakata, in ba haka ba kuwa duk abin da ya same su to su kuka da kansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “An nusar da Hukumar Kula da Hada-Hadar Hannayen Jari game da shafin intanet da kamfanin Binance ke gudanarwa, inda yake neman ’yan Najeriya da su zuba jari kan harkar hada-hadar kudin intanet na cyrpto a shafin nasa da wasu manhajojin wayar hannu.

Kan haka ne hukumar ke bayyana wa ’yan Najeriya cewa “kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ ba shi da rajista da ita, kuma baya aiki da dokokin Hukumar Kula da Hannayen Jari ta SEC, don haka duk abin da ya samu mutumin da ke mu’amala da kamfanin to ya kuka da kansa”.

Hukumar ta kuma shawarci ’yan kasar da su guji zuba jari a harkar hada-hadar kudaden intanet ta crypto a kamfanonin da ba su da rajista da hukumar.

Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriyar ta bukaci kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ da ya gaggauta dakatar da ayyukansa a fadin kasar.

SEC ta kuma ce za ta bayyana matakan ladabtarwa da za ta dauka kan kamfanin da wasu takwarorinsa marasa rajista a kasar.

Ta kara da cewa za ta yi aiki tare da hukumomin da lamarin ya shafa a kasar domin daukar mataki game da batun.

A makon da ya gabata ne dai Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Amurka ta shigar da karar kamfanin na Binance a gaban kotu.

A ranar Alhamis ne kuma kamfanin ya ce ya dakatar da hada-hada da kudin dala na Amurka bayan matakin da gwamnatin kasar ta dauka a kansa.

Wannan mataki dai ka iya kawo cikas ga kasuwar hada-hadar kudi ta intanet wato crypto a Najeriya, musamman ganin cewa a baya-bayan hukumar ta SEC ta haramta ayyukan kamfanin Paxful.