Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta gabatar da Tigran Gambaryan, jami’in Kamfanin Binance a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin damfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, manajan Binance a Afirka wanda ya nemi tserewa a kwanakin baya.
Yayin da ake dakon kamo Anjarwalla wanda a makonnin da suka gabata ya tsere, gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin a gurfanar Gambaryan a kotu, ranar Alhamis.
- Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin shari’a kan Binance
- Jami’in Binance ya tsere daga hannun mahukuntan Nijeriya
Sai dai Kotu ta ɗage sauraron ƙarar na yau Alhamis saboda Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) ta gaza yi miƙa ƙunshin tuhume-tuhumen da take yi wa Mista Gambaryan.
Wakilinmu da ya ziyarci Kotun ya aiko da hotunan yadda zaman ya kasance kamar haka: