Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce har yanzu yana nan a kan bakarsa ta sayar wa ’yan kasuwa da matatun man Najeriya muddin ya lashe zaben.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa ta musamman da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), yayin ziyarar da ya kai birnin Washington D.C na kasar.
- An harbi tsohon Fira Ministan Pakistan, Imran Khan
- Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta cafke mutum 130 a Kaduna
Ya ce, “Har yanzu matsayina bai canza ba, na riga na fada tun a shekarun baya, zan sayar da su. Saboda idan ka sayarwa da ’yan kasuwa, za su sa su rika aiki yadda ya kamata.”
Dangane da satar danyen mai a Kudancin Najeriya kuwa, tsohon Mataimakin Shugaban na Najeriya ya yi alkawarin kawo karshen matsalar da zarar ya zama Shugaban Kasa.
“Wannan matsala ce ta daban da za mu duba yiwuwar yin amfani da karfin gwamnati wajen magance ta, saboda dole a sami hadin gwiwa tsakanin Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) da jami’an tsaro, wadanda su ne ke da alhakin tsare wadannan bututan man fetur din,” inji shi.
Najeriya dai a yanzu haka tana da matatun mai guda hudu a Kaduna da Warri da Fatakwal, wadanda ba sa aiki kwata-kwata.
A sakamakon haka, galibin tataccen man da ake amfani da shi a kasar daga ketare ake shigo da shi.