Shugaban Amurka Joe Biden, ya gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari da wasu takwarorinsa na kasashe 39 shiga taron tattauna matsalar sauyin yanayi da ta addabi duniya.
Kamar yadda Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito, taron na kwanaki biyu wanda za a gudanar da zummar shawo kan matsalar sauyin yanayi, zai gudana ne ta kafar bidiyo a Intanet.
- An sayar da kalmomin farko da aka wallafa a shafin Twitter kan dala miliyan 2.9
- Shugaban Chadi ya ziyarci Buhari a Abuja
Taron zai jaddada dawowar Amurka sahun gaba wajen yaki da sauyin yanayin sabanin matsayin da kasar ta kasance a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Donald Trump.
Sanarwar da Fadar White House ta fitar ta ce za a yi taron ne a tsakanin ranakun 22 zuwa 23 ga watan Afrilu wanda ake fatan zai kara kaimi a yunkurin kasashen duniya na shawo kan wannan matsala.
Ana kuma sa ran taron zai bayar da muhimmanci wajen ganin dabarun magance matsalar sun taimaka wajen samar da ayyukan yi da dabarun fasaha ga kasahen da ke fuskantar radadin sauyin yanayi.
Kadan daga cikin shugabannin duniya da za su shiga taron akwai Shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha, Shugaban China XI Jinping, Shugabar Jamus, Angela Merkel, Emmanuel Macron na Faransa da kuma Borris Johnson, Firaiministan Birtaniya.