✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauro da dansa

Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Rannan sai uban ya ce masa: “Ya kamata yau ka tashi kai…

Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Rannan sai uban ya ce masa: “Ya kamata yau ka tashi kai kadai, domin in ga kwarewarka.” Dan saurayin sauron nan ya bude fiffikensa ya tashi sama, ya yi shawagi. Bayan ya dawo, ya sauka, sai uban ya tambaye shi cewa: “Shin ya ka ji lokacin da ka tashi?” Cikin farin ciki saurayin sauron ya gaya wa babansa cewa: “Wato abin da ya fi burge ni, shi ne irin yadda na ga duk inda na wuce mutane na yi mini tafi.” Uban ya klale shi ya yi murmushi ya ce: “ Yaro, ai ba tafi suke maka ba, kashe ka suke so su yi.”

Daga Fatuhu Mustapha

 

Tambaya ba amsa

Wani sabon malami ne aka kawo shi wata makarantar sakandare, domin ya koyar da Tarihi. Shigarsa aji ke da wuya  sai ya ce wa wani dalibin:  “Tashi tsaye, shin wa y akashe Murtala Ramat Muhammad?” Dalibin ya ce:  “Malam, ban sani ba wallahi.” Sai ya tambayi dalibi na biyu, shi kuma sai ya ce: “Malam, ranar da aka kashe shi ban zo makaranta ba.” Dalibi na uku kuma ya ce: “Wallahi ni sabon zuwa ne makarantar nan.” Malamin ransa ya baci, sai ya kirawo shugaban makaranta ajin, ya gaya masa abin da ya faru, sai shugaban makaranta ya tambayi ’yan ajin ga baki dayansu, suka ce ba su sani ba. Sai shugaban makaranta ya juwo, ya ce wa malamin: “Kai malam, ka tabbata da gaske a nan ajin aka kashe Murtala Ramat Muhammad?”

Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300

 

Da da uba

Wani Bakano ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yanda hirarsu takasance: Baba: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji ana cewa dalibai suna ta zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kar ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku. Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bisu ba baba.” Baba: Yauwa dan arziki sai anjima. Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce da shi: “Wai mene ne dalilin yin wannan zanga-zangar? Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300. Baba: Iye! Yanzu kai kana ina? Yaro: Ina kwance a daki. Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!

Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300

 

Na dagula

Wani kuturu ne ya je sayen garin kwaki wajen wani Inyamuri, sai ya sa dungun hannunsa ya debi kadan da nufin dandanawa. Sai Inyamuri ya kwashe daidai wajen da ya sa hannu ya zubar. Sai haush ya kama kuturu, sai ya tura dungun hannun duka cikin buhun garin, ya ce “Na dagula, na dagula.”

Sayyada Fatima Muhammad Galadima Bichi