Wani saurayi dan shekara 16 mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a kauyen Kuki da ke Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano.
Har yanzu dai ba a gano dalilin wannan danyen aiki da saurayin ya yi ba.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai ya fitar, ya mika rahoton afkuwar lamarin ga Mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, a yayin zaman fada a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa, Sarkin ya ba da umarnin a kai rahoton ga ’yan sanda da ke masarautar domin gudanar da bincike mai zurfi kan musabbabin mutuwar saurayin.
Sai dai da aka tuntubi jami’in huldar don jin karin bayani kan lamarin, ya shaida wa wakilinmu cewa, hakimin kauyen ya yi wa mahaifin marigayin tambayoyi kan ko yaron yana shaye-shaye ko kuma ya nada tabin hankali.
“Sarkin ya damu da lamarin, ya tambayi Hakimin ko saurayin yana shan miyagun kwayoyi.
“Ya kuma tambayi mahaifin ko yana da matsalar tabin hankali ne ko kuma ya samu sabani ne da wani, amma mahaifin ya ce ba a yi masa komai ba. Ya kuma ce ba ya shaye-shaye,” in ji Faragai.
Ya kara da cewa, Sarkin ya umarci Hakiman Karamar Hukumar da su gudanar da addu’o’i neman agajin Allah kan gujewa faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
A lokacin hada wannan rahoton, an nemi jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa amma bai iya amsa kiran wayarsa ba.