✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura maki 4 Real Madrid ta lashe Gasar Laliga

Real Madrid ta fara jiyo kamshin kofin Laligar bana.

Real Madrid na ci gaba da kusantar lashe gasar Laliga ta  bana, bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Osasuna da ci 3 da 1 a daren ranar Laraba.

Madrid ta samu nasarar zura kwallaye uku ta hannun ’yan wasanta; Alaba, Asensio da kuma Lucas Vazquez.

Sai dai hazikin dan wasan kungiyar da ke jan ragamarta a kodayaushe, Karim Benzema, bai samu zura kwallo a wasan ba, inda ya zubar da bugun fenariti biyu a cikin minti bakwai da Real Madrid ta samu.

Yanzu haka dai kungiyar na neman akalla maki hudu daga jerin wasannin da suka rage mata don zama zakaran gasar ta bana.

Yanzu haka dai Benzema ne ke kan gaba wajen zura kwallaye a raga da kwallo 25 a gasar ta Laligar bana.