✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura kiris jiragen Emirates su dawo aiki a Najeriya —Keyamo

Kamfanin jirgin ya dakatar da jigilarda a Najeriya sakamakon bashin kudade da yake bi.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da harkokinsa a Najeriya nan ba da jimawa ba.

Keyamo ya ce ya gana da wasu manyan masu ruwa da tsaki na Hadaddiyar Daular Larabawa kuma nan gaba za su bayyana ainihin ranar da za su fara aiki.

Ministan ya ce a ganawar sun yi magana da wakilan kamfanin Emirates dangane da tashinsu daga Dubai zuwa Najeriya, da kuma magance matsalolin da suka faru a baya.

Ya kara da cewa gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu na kokari kan sake dawowar jigilar jiragen.

Keyamo ya kuma bayyana cewa ya ziyarci manyan masana’antun sufurin jiragen sama a fadin duniya don kulla alaka tsakaninsu da Najeriya.

A watan Oktoban 2022, kamfanin Emirates ya dakatar da harkokinsa a Najeriya saboda kasa biyan sa wasu kudade da yake bi.

Sau biyu kamfanin jirgin ya dakatar da aikinsa a Najeriya a shekarar da ta gabata, na farko a watan Agustan 2022, saboda kudadensa Dala miliyan 85 da suka makale a Najeriya.

Bayan da Tinubu ya ziyarci UAE a watan Satumba, Ajuri Ngelale, mai magana da yawunsa, ya ce an dage haramcin bizar kasar ga ’yan Najeriya kuma Emirates tare da Etihad za su dawo da zirga-zirgar jiragen samansu a Najeriya.

Daga baya mahukuntan UAE sun musanta ikirarin Ngelale, lamarin da ya janyo suka ga fadar shugaban kasa.