Wani barawo da aka kama a cikin wani gida, ya tsallake rijiya da baya yayin da fusatattun matasa suka yi kokarin hallaka shi.
Wannan lamari ya faru ne a unguwar Lugbe da ke kan babbar hanyar zuwa Filin Jirgin Saman Abuja da safiyar ranar Asabar.
- An kama barawon sadakar N600,000 da coci ta tara
- Kotu ta yanke wa barawon doya 5 wata 6 a gidan yari
Barawon ya shiga wani gida ne a Layin Masallacin Juma’a na ’yan Darika da kimanin karfe 5:30 asuba bayan idar da Sallah.
Cewar wanda ya kama barawon Abubakar J-Man, “Na fito da buta zan debi ruwa sai na ga barawon a tube daga shi sai gajeren wando da wuka a kugunsa yana leka wundon wani daki.
“Ganin ba ni da makami sai na yi ihu, na kuma yi hanzarin nemo makami, kafin in ankara, ya gudu, sai ni da sauran ’yan gidan muka bi shi, daga karshe Allah Ya taimaka muka cim masa a kusa da makaranta.”
Wani mazaunin gidan Isa Lawan ya ce, kusan sau goma ana haurawa ana yi musu sata, wanda kuma barawon yake lekawa dakin sa kuwa, ba a jima da dauke masa kwamfuta da jakarsa ba a dakin, kuma suna zargin shi ne.
Fusattun mutanen unguwar ne dauke da makami suka yi kokarin hallaka barawon, da kyar dattawan unguwar suka hana, a inda daga karshe suka kai shi ofishin ’yan banga na unguwar.
Aminiya ta tuntubi Salisu Kwamanda wanda ya tabbatar da faruwa lamarin, ya kuma ce, sun mika wanda ake zargi ga ofishin ’yan sanda na Lugbe, don daukar matakin da ya dace.