Tsoho mai ran karfe – sau biyu daya daga cikin mutanen da suka dade a harkar fim yana tsallake rijiyar da baya saboda rawar da ya taka a wani shiri – Salaha misali – ko kuma yayin da yake bakin aiki.
Da Auta Baita aka san shi a shirin ‘Kwana Casa’in’; amma ba wannan ba ne karo na farko da Musa Mohammed Abdullahi ya fito a matsayin babban dan siyasa a fim.
A wannan hirar da ya yi da Aminiya, dadadden jarumin mai shekara kusan 70 ya fadi yadda ya yi arangama da kada a lokeshin da yadda aka kusa a zubar da jininsa saboda fim.