✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta yi dokar hana yada Hadisan karya

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar cibiyar Addinin Musulunci da za ta takaita tsattsauran ra’ayin Musulunci da kuma ‘yan ta’adda da ke jirkita ma’anar…

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar cibiyar Addinin Musulunci da za ta takaita tsattsauran ra’ayin Musulunci da kuma ‘yan ta’adda da ke jirkita ma’anar wasu Hadisai domin samun damar aikata barna.

Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz Al Saud ne ya sanya hannu kan wannan kudurin dokar, wacce za ta bayar da damar kafa wannan cibiya. Kuma dokar ta bayyana cewa cibiyar za ta kasance ne a birnin Madinah.

Haka kuma za a dauki Malamai kuma masana addinin Musulunci daga sassan duniya daban-daban wadanda za su jagoranci ayyukan cibiyar. A yayin bayyana dalilan dokar, mahukunta a kasar sun ce ‘yan ta’adda na gurbata fassarar wasu hadisan Annabi Muhammad (SAW), domin kafa hujja da su wajen munanan ayyukan da suke yi.

Za kuma su rika aiki tukuru domin zakulo tare da kawar da duk wani hadisi da ke da alamun kage ko wanda aka sauyawa ma’ana domin kafa hujjojin ta da fitina.

Koda yake an dade ana zargin kungiyoyin masu tayar da kayar baya a duniya wajen sauya ma’anar ayoyin Alkur’ani da Hadisai domin kafa hujja kan ta’addancin da suke aikatawa. Amma wasu na zargin cewa wadannan sauye-sauye ba za su rasa nasaba da matsin lambar da Amurka ke wa Saudiyyar ba, na ganin ta sauya yadda take tafiyar da al’amuran addini a kasar. Amma jami’an Saudiyya sun musanta irin wadannan zarge-zarge da suka kira shaci-fadi. Baya ga Alkur’ani Mai Girma, ilimin Hadisai dai shi ne mataki na biyu na fahimtar Addinin Musulunci, wadanda suka kunshi kalaman Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) kan sha’anin addini a fannoni daban-daban da suka hada da hukunce-hukunce da kuma mu’amala, amma sai dai ana samun wasu Hadisan da ake jirkita ma’anarsu, ko kuma hadisan karya wadanda ba su da asali.

Bisa wadannan dalilai ne kasar ta Saudiyya da ma sauran kasashen musulmin duniya ke ci gaba da nuna damuwa. Kawo yanzu dai ba a bayyana cikakken tsarin da za a bi wurin aiwatar da ayyukan cibiyar da kuma lokacin da za ta fara aiki ba.