✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta zartar wa dan kasarta hukuncin kisa kan ta’addanci

An zartar wa al-Asmari hukuncin kisa kan laifin kafa kungiyar ta'addanci

Gwamnatin Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa ga wani dan kasar da kotu ta kama da laifin kafawa da kuma jagorantar kungiyar ta’addanci da kuma kulla kawance da wasu kungiyoyin ta’addanci da nufin kai hare-hare a cikin kasar.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an zartar wa mutumin mai suna Yasser bin Mohammed al-Asmari hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan kotunan kasar sun tabbatar da hukuncin a kansa.

Ma’aikatar ta bayyana cewa laifukan al-Asmari sun hada da “kafa kuniygar ta’addanci da nufin kai hare-hare musamman ga jami’an tsaro a cikin kasar Saudia.”

“Ya kuma yi mubaya’a ga jagoran wata kungiyar,”  ta’addanci sannan ya kulla kawance da wasu kungiyoyin ta’addanci inda ya bukaci taimakonsu, in ji sanarwar ma’aiakatar.

An kuma sami al-Asmari da laifin bayar da mafaka ga masu tsattsauran ra’ayi da kuma daukar su aiki da kuma ba su horo a kan hada abubuwan fashewa, gami da ba su umarnin inda za su kai hare-hare.

Ma’aikatar ta ce al-Asmari ya kuma dauki makami a yankunan da ke fama da rikici, tare da bukatar ‘yan dabarsa da su same shi a can.