✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta tsare mutum 17,615 da suka yi yunkurin Aikin Hajji babu izini

An kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.

Hukumomin Saudiya sun kama tare da tsare mutum 17,615 da suka yi yunkurin yin Aikin Hajjin ba tare da izini ba.

Shugaban Kwamitin Tsaro na Aikin Hajjin bana, Laftanar Janar Muhammad Al Bassami ne ya bayyana hakan kamar yadda Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Al Bassami ya bayyana cewa 9,509 daga cikinsu mutane ne da suka saba ka’idar bizar aiki da ta zaman kasar.

Ya ce an kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.

Al-Bassami ya ce hukumomin kasar kuma sun tisa keyar mutum 202,999 da suka yi yunkurin shiga kasar don gudanar da Aikin Hajjin ba tare da izini ba.

Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin ya kuma yaba wa askarawan kasar bisa jajircewa da ya ce sun yi a lokacin gudanar da wannan gagarumin aiki cikin kwarewar aiki da basira.

Dokokin Saudiyya sun tanadi cewa duk mutumin da ke zaune a kasar, dole ne ya nemi izinin hukumomi idan yana son gudanar da Aikin Hajji.