✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jinina zai iya hawa da ban ci zaben Sanata ba – Oshiomhole

“Da a ce na fadi, jinina zai iya hawa, idan ma ban mutu ba ke nan”

Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya ce jininsa zai iya hawa da a ce ya fadi zaben takarar da ya tsaya ta Sanatan Edo ta Arewa.

Ya bayyana hakan ne ranar Asabar, yayin wata liyafar godiya ta bayan rantsuwa da abokan arziki suka shirya masa.

An yi taron ne a mahaifarsa da ke Iyamho a Karamar Hukumar Etsako da ke Jihar.

A cewarsa, “Da ba ku zabe ni ba, da jinina ya hau zuwa 240/0360; idan ma ban mutu ba ke nan.

“Dalili kuwa shi ne murnar da abokan adawa za su rika yi sai sun yi kamar su shigo su balle kofar gidana su babballa kasusuwana, amma kuka tsaya kai da fata wajen ganin haka bai faru ba,” in ji shi.

Oshiomhole, wanda kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC ne na kasa, ya ce ya gode Allah da bai fadi zabe ya kunyata kamar sauran tsofaffin Gwamnoni ba.

Ya kuma yaba wa mutanen mazabar tasa saboda damar da suka ba shi don ya wakilce su a Majalisar Dattijan Najeriya da kuma Bola Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya.

Oshiomhole dai ya lashe zaben kujerar Sanatan Edo ta Arewa ne a karkashin jam’iyyyar APC a babban zaben 2023 da ya gabata.