✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta sahale wa mata sauke farali ba tare da muharrami ba

Wannan ya kawo karshen cece-kucen da ake yi kan batun.

Kasar Saudiyya ta ce daga yanzu babu bukatar rakiyar muharrami ga mata masu zuwa Kasa Mai Tsarki don aikin Hajji da Umrah.

Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dokta Tawfiq Al-Rabiah ne ya sanar da hakan domin kawo karshen cece-kucen da ake yi kan batun.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Al-Kahira, Ministan ya ce ko daga ina maniyyaciya take a sassan duniya za ta iya tafiya Hajji ko Umrah ba tare da rakiyar muharrami ba.

Daga nan Al-Rabiah ya ce, babu wata kayyadewa dangane da adadin maniyyatan da za a bari su je Umrah daga sassan duniya.

Kazalika, ya ce aikin fadada Masallacin Harami da ke Makka ya lakume biliyan SR200, kuma wannan shi ne aikin fadada masallacin mafi girma wanda aka taba yi.