Masarautar Saudiyya karkashin jagorancin masu da kula masallatan harami, ta dauki nauyin raba wasu tagwaye da aka haifa manne da juna a Jihar Kano.
A wannan Litinin din ce dai aka garzaya da jariran tare da mahaifiyarsu da wasu yan uwa zuwa kasa mai tsarki domin yi musu tiyata a Riyadh, babban birnin Saudiyya.
- FIFA ta dakatar da tsohon shugaban kwallon Sifaniya Luis Rubiales
- Mutum 14 sun mutu, 50 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a Indiya
Bayanai sun ce Cibiyar Jin Kai ta Sarki Salman ce za ta jibinci lamuran yi wa Hasana da Husainar tiyatar da ke manne da juna ta kirji da ake ganin aikin yana tattare da kalubale.
A cewar Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Najeriya, labarin tagwayen ya dauki hankalinsu miliyoyin jama’a matuƙa a fadin duniya, dalili ke nan da aka nemo kwararrun likitoci da za su yi musu tiyatar don ceton rayuwarsu wajen samun makoma mai inganci .
Za a tanadar wa ’yan uwan tagwayen masauki a birnin na Riyadh kusa da Cibiyar Lafiya ta Sarki Abdulaziz inda za a yi musu aikin, a cewar Ofishin Jakadancin.
Sanarwar ta ce wannan wani yunƙuri ne da ke kara tabbatar da ƙudirin Saudiyya na gudanar da ayyukan jin kai ga mabukata ba tare da la’akari da asalinsu ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, Saudiyya dai ta shahara a fagen inganta lafiyar jama’a daga sassan duniya daban-daban, ciki har da Shirin Raba Jariran Da Aka Haifa a Manne da Juna.
A shekarar 1990 ce aka assasa shirin raba jariran da aka haifa manne da juna a Saudiyya, inda kawo yanzu an samu nasarar raba jerin tagwaye 59 da aka haifa manne da juna daga kasashe 24.
Da yake yi wa iyalan tagwayen bankwana a filin jirgin Saman na Malam Aminu Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, sun yi musu addu’ar samun sauki da fatan samun nasarar aikin.