Wata maniyyaciya daga Najeriya ta haifi jariri na farko a lokacin aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.
Mai jegon ta haihu dan, wanda aka sanyan masa Muhammad ne a Asibitin Mata da Kananan Yara na Makkah a ranar Talata.
A halin da ake ciki mai jegon, mainshekaru 30 daga Jihar Borno tare da jaririnta Muhammad suna samun kulawa ta musamman a wurin likitoci a asibitin da ke birnin Makkah.
Kafar yada labarai ta Arab News ya ruwaito cewa nakuda ta taso wa Hajiyar ce kimanin wata biyu kafin lokacin haihuwa.
- Kotu ta tsare magidanci kan gwada ƙarfi a kan matarsa a Kano
- Uwa ta ƙone ɗanta ta raunata ‘yar uwarta da wuƙa a Bayelsa
Mai jegon, ta bayyana godiyarta ga Allah fara sauka lafiya da kuma kulawar da ta samu a asibitin.
Hukumomi sukan hana masu juna biyu zuwa aikin Hajji duk da cewa Musulunci bai haramta ba.
Akan hana su ne lura da wahalhalun da ke tattare da aikin Hajji, wanda ke iya shafar lafiyar mai juna biyu da abin da take dauke da shi.
A kan haka ne ake tantance mata domin tabbatar da ba sa sauke da juna biyu kafin tafiya aikin Hajji.
Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta tabbatar da haihuwar amma ta ce akwai yiwuwar mai jegon ta kauce wa gwajin juna biyu da aka yi wa maniyyata.
A lokacin aikin Hajjin 2023 alhazan Najeriya masu dauke da juna biyu 75 ne suka ga likita a Saudiyya.