Hukumomin Saudiyya sun yi ragin kudin Hajji ga maniyyatan da za su sauke farali a bana, 2024.
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar cewa shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya nemo ragin ragin da aka yi ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai a Saudiyya.
Kakakin NACHON, Fatima Sanda Usara ta sanar a ranar Laraba cewa a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal daga 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.
“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.
Sai dai duk da haka, sanarwar ba ta bayyana ko NAHCON za ta yi wa maniyyayatan Najeriya ragin kudin kujera daga Naira miliyan 4.5 da ta sanar tun da farko ba.
Kazalika ana hasashen duk da saukin da wannan saukin da Saudiyya ta yi, da wuya maniyyayatan Najeriya su shaida sauƙin — daga Naira miliyan 3 da suka biya a 2023 — sakamakon tashin farashin Dala.
Farashin kudaden kasashen waje musamman Dala sai kara karuwa yake a Najeriya, lamarin da ke kara haifar da tsadar rayuwa a kasar.
Akasari ana biyan kudin aikin Hajji da sauran huldodin kasa da kasa, kamar aikin Hajji da sauransu ne da Dala ko sauran kudaden kasashen waje.
Faduwar darajar kudin Najeriya, Naira da tashin dala da danginsa a kasar ta sa a duk shekara kudin aikin Hajji karuwa.
A sakamakon haka ne aka samu karin kashi 50 a kudin aikin Hajjin 2024 a kan na 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu taguwar maniyyayatan Najeriya da za su sauke farali a bana a sakamakon tsadar kudin kujera.