✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami

Hukumomin Saudiyya sun ce ba za su lamunci wannan wuce gona da iri ba.

Rahotonin da ke fitowa daga kasar Saudiyya dai sun yi nuni da cewa hukumomi a kasar sun cafke wasu ’yan Najeriya da ake zarginsu da wuce gona da iri wajen shiga tare da daga hotunan wasu ’yan siyasa da ke neman tsayawa takarar shugabanci a gaban dakin Ka’aba.

’Yan Najeriya wadanda suka samu damar kai ziyarar aikin Umrah na bana a kasar saudiyya sun yi tsokaci game da zargin cafke wasu ’yan kasar da hukumomin Saudiyar suka yi bisa laifin daga hotunan ’yan siyasa da ke neman takarar shugabanci a Najeriya a Harami yayin gudanar da dawafi a gaban dakin Ka’aba.

Wani Murtala Adamu Jega wanda Muryar Amurka ta tattauna da shi ya ce shi ganau ne na lamarin.

Ya ce lamarin na iya bata sunan kasar wanda kuma kamata ya yi a ce masu aikin Umrar sun dauki lokaci su yi addu’a a samu zaman lafiya da tsaro a kasar ba yi wa masu neman tsayawa takara addu’a ba.

Wasu na ganin ’yan siyasar ne suka biya wa magoya bayansu kudin zuwa aikin Umrah da nufin rokon Allah don samun nasara a babban zaben kasar da ke tafe.

A halin da ake ciki dai majiyar daga Saudiya ta bayyana cewa wadanda aka kama suna hannun mahukunta kasar, karkashin kulawar askarawa domin gurfanar da su gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata.

Tun dai a cikin watan Ramadana aka yi ta hango yadda wasu ’yan Najeriya da suka dinga tallar ’yan siyasar kasarsu a garin makkah, lamarin da hukumomi a kasar suka ce baza su lamunta ba.