Saudiyya ta tattauna da shugabannin Iran da kuma Turkiyya kan yadda za a kawo karshen sabon yakin Isra’ila da kungiyar Falasɗinawa ta Hamas.
A tattaunawarsu da Shugaba Ebrahim Raisi na Iran, Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed Bin Salman ya “jaddada muhimmancin kawo karshen laifukan yaki da Isra’ila ke aikatawa a yankin Falasdinawa na Zirin Gaza.”
Mohammed Bin Salman wanda Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya kira ta waya a ranar Laraba, ya ce Saudiyya tana “tuntubar da duk masu ruwa da tsaki na duniya da kuma Gabas ta Tsakiya da nufinn ganin an kawo karshen yakin.”
A ranar ce kuma ya yi wata ganawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya inda Yariman ya ce Saudiyya “na yin gagarumin fadi tashi don ganin kasashen Gabas ta Tsakiya da sauran wurare su taimaka wajen kawo karshen yakin Gaza na yanzu.”
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito cewa Mohammed Bin Salman ya kuma jaddada “cikakkiyar goyon bayan Saudiyya ga yunkurin Falasdinawa sun samu kasarsu mai cikakkiyar ’yanci.”
Tattaunawarsa ta waya da Shugaba Raisi na Iran ita ce irinta na farko tun bayan da kasashen biyu masu zaman doya da manja sun fara tattaunawa domin sasanta tsakaninsu.
Hannun agogo ya koma baya
Iran kuma ta jima tana taimaka wa kungiyar Hama da kudade da makamai da kuma horon soji, amma ta ce ba ta hannu a harin kungiyar na ranar Asabar.
Masana na ganin sabon rikicin ya kawo koma baya ga nasarar da aka samu a yunkurin da Amurka ke jagoranta na daidaita tsakanin Saudiyya da Isra’ila.
A yayin tattaunawar sasanta kasashen biyu, Saudiyya ta samu amincewar fara shirin bunkasa bangaren makamashin nukiya ta fuskar da ba na soji ba.
A watan Maris China ta jagoranci sasanta Saudiyya da Iran, da nufin kawo karshen zaman doya da manjan shekara bakwai a tsakaninsu.