Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya sama da sau 50 daga harin ’yan Boko Haram suke kai masa da nufin hallaka shi.
Zulum wanda ya bayyana haka yayin ziyarar da ya kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa kungiyar ta kashe sama da mutum 100,000 a jiharsa.
A cewarsa, bayan mutanen da kungiyar ta kashe ’yan asalin jihar Borno, ta kuma jikkata wasu da dama cikin shekara 12 da ta yi tana ayyukan ta’addanci.
Gwamnan ya sanar cewa ya zuwa yanzu mayakan Boko Haram 2,600 ne suka tuba, suka mika kansu ga Gwamnatin Jihar Borno, cikinsu har da mata da kananan yara.
Ya kuma bayyana cewa wadansu daga cikin tubabbun ’yan Boko Haram din da suka hada da mata da kananan yara an shigar da su kungiyar ce ta karfin tsiya.
Zulum wanda ya ce gwamnatinsa ba za ta ba wa wadanda suka ajiye makamai kudi ba, ya kara da cewa ya kai wa Shugaba Buhari ziyara ce domin tattaunawa kan makomar tubabbun ’yan Boko Haram din.
Tuni mutane da dama daga cikin ’yan Najeriya suke ta muhawara kan ko tubabbun ’yan Boko Haram din sun cancanci a yafe musu.
Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ba za ta hukunta su ba, saboda yin hakan ya saba wa dokar yaki ta Majalisar Dinkin Duniya.