Wata mata da ta sace jakunkunan kawayenta biyu a wurin biki za ta wata 10 a gidan yari.
A ranar Laraba ne kotu ta yanke wa barauniyar hukuncin daurin wata 10 a gidan yari bayan ta amsa laifukanta na sata, yaudara da kuma cuta.
- Ana kama matukan jirgi da mataimakansu 40 sun sha giya kafin tashi sama
- Lyon ta dakatar da dan wasanta saboda tsananin banka tusa
Kotun da ke zamanta a yankin Mararaba da ke Jihar Nasarawa ta umarci barauniyar ta biya kawayen nata N37,000 sannan ta sauya hali.
Alkalin Babbar Kotun Yankin, Malam Hassan Ishaq, ya kuma ba ta zabin biyan tarar N25,000 ko kuma zaman gidan.
Tun da farko, lauyan masu mai gabatar da kara, Olarewaju Osho, ya ce a ranar 5 ga watan Afrilu ne masu karar Andrew Aloysius da Felicia Levi suka kai rahoton kuruciyar berar da kawar tasu ta yi musu ga ofishin ’yan sanda da ke Nyanya.
Ya ce a watan Fabrairu, barauniyar ta sace karamar jakar katarwa da kayan da ke ciki a lokacin wani bikin zagayowar ranar haihuwa da aka gudanar a gidan casu na ‘Emzy Garden’ da ke Nyanya.
A cewarsa, akwai wayar kirar Tecno wadda kudinta ya kai N30,000 da kuma tsabar kudi N7,000 a cikin jakar da ta dauke.
Mai gabatar da karar ya ce a lokacin bincike, wadda ake zargin ta amsa cewa ita ce da sace wayar ta sayar N6,000 amma ta kashe kudin.
Laifin a cewarsa, ya saba da Sashe na 312 da kuma 287 na dokar fenal kod.