Wata kotun majistare dake zamanta a garin Kaduna ta yanke wa bakanike, Amos Dauda hukuncin bulala 15 saboda samun sa da laifin satar wayar salula kirar iPhone da kudinta ya kai kusan N150,000.
Kotun dai ta daure Amos, mazaunin unguwar Barnawa a Kaduna mai kimanin shekaru 20 da haihuwa hukuncin bayan an zarge shi da laifin sata da keta iyaka.
- Kotu ta tsare Sanata Ali Ndume a kurkuku
- Dukan dan takara: Kotu ta sa a kamo Shugaban Karamar Hukumar Gaya
Sai dai wanda ake zargin bai yi musu ba inda nan take ya amsa aikata laifin tare da neman sassaucin kotun.
Alkalin kotun, mai shari’a Ibrahim Emmanuel ya yanke masa hukuncin bulala 15 tare da hukuncin share harabar kotun a matsayin horo.
Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara Insfekta Leo Chidi ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Stephen Francis ne ya kai karar matashin ofishin ‘yan sandan na Gabasawa a ranar 15 ga watan Nuwamba.
Ya ce Amos din ya haura gidan mai karar lokacin da yake bacci sannan ya dauke wayar da darajarta ta kai N150,000.
Dan sandan ya ce an kama Amos din ne lokacin da yake kokarin tserewa daga gidan bayan daukar wayar.
A cewarsa, laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 257 da na 271 na kundin dokokin Penal Code na jihar Kaduna na 2017.