✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar ruwan gora ta ja masa daurin wata 3 a kurkuku

Kotun ta yanke masa hukunci bayan ya amsa cewa ya saci kwali shida na ruwan gora a wani kanti

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin wata uku a gidan yari saboda samun shi da laifin satar ruwan gora a wani kanti.

Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a Jihar Ekiti ta yanke hukuncin ne bayan mutumin mai shekara 38 da aka gurfanar a gabanta kan zargin satar kwali shida na ruwan gora  ya amsa laifin.

Bayan yanke hukuncin, alkalin kotun, Misis Mrs Titilayo Ola-Olorun, ta ba wa mutumin zabin biyan tarar Naira dubu 10.

Tun da farko, a yayin da yake gabatar da wanda ake zargin, dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Johnson Okunade, ya shaida wa kotun cewa matashin ya shiga shagon wani mai suna Alhaji Babalola Isiaka ne, sannan ya sace kwali shida na ruwan gora, wanda kudinsu ya kai N4,500.