Hukumar Yaki da Yi Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta kama dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Ismaila Yusuf Atumeyi, bisa zargin sa da almundahanar miliyan N326 da kuma Dala 140,500.
EFCC ta kama dan takarar, mai neman wakiltar mazabar Ankpa karkashin Jam’iyar NNPP ne ranar Lahadi, tare da wani mai suna Joshua Dominc, hadi da wani fitaccen dan damfara, a samamen da hukumar ta kai a unguwar Gwarinpa da ke Abuja.
- Farashin amfanin gona a kasuwannin Arewa
- Mutum 110 sun mutu sakamakon ambaliya da zabtarewar kasa a Philippine
Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwajeran ya sanar da Aminiya cewa baya ga wadannan mutanen, an kamo wani tsohon ma’aikacin Banki da shi ma ke da alaka da damfarar.
Uwajeran ya ce Femi ne ya bai wa sauran bayanan sirri kan yadda za su yi wa bankin kutse ta intanet su sace kudaden, inda suka je har gida suka dauko shi ranar Talata a wani Otel da ke Legas.
“Bayan kamo su mun binciki gidansa da ke Rukunin Gidajen Morgan inda muka samu Dala 470,000.
“Mun kamo su ne bayan da muka kwashe watanni muna bincike kan kutsen da ake yiwa Bankin har aka kwashe musu biliyan N1.4.
“Sun kuma bayyana mana cewa sun tura miliyan N887 zuwa asusun kamfanin Fav Oil, daga nan kuma aka tura wa wasu ’yan canji da dillalan motoci suka sauya su zuwa Dala da kuma sayo motoci,” in ji Uwajaen.
Ya ce an kama su da motoci guda biyu kirar Range Rover a Abuja, kuma da zarar an kammala bincike za a mika su kotu.