✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Satar Mutane ta ragu da kashi 28 a watan Agusta —Rahoto

An samu rahoton satar mutane sau 599 a fadin kasar.

Yawan sace-sacen jama’a ya ragu da kashi 28 cikin dari a watan Agustan bana idan an kwatanta da alkaluman watan Yuli, a cewar wani rahoton tsaro.

Wani kamfanin tsaro mai zaman kansa ne ya wallafa rahoton cikin jerin rahotanni da ya saba fitarwa lokaci-lokaci.

Wakilinmu wanda ya yi nazari kan rahoton, ya bayyana cewa, an samu karuwar kashi 49 na adadin wadanda suka jikkata a sanadiyar sace-sacen mutane, idan aka kwatanta da alkaluman watan Yuli.

Rahoton bai bayyana takamaiman wadanda aka hallaka ba, sai dai ya nuna an samu karuwar kai-komon sojojin don magance matsalar a baya-bayan, a inda suke fafatawa da ‘yan Boko Haram da ISWAP.

Haka kuma rahoton ya nuna cewa, jami’an tsaro sun kara kaimi wajen dakile ayyukan yan awaren Biyafara na IPOB da masu satar mutane da kuma sauran kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, an samu rahoton satar mutane sau 599 a fadin kasar, wanda hakan ta kai ga kisan mutane 859, da kuma karin garkuwa da wasu mutanen 380 don neman kudin fansa a kananan hukumomi 262 da ke jihohi 36 da kuma Abuja.

Batun kazar-kazar din jami’an tsaro gami da ikirarin nasara da gwamnatoci ke ta yi kan ‘yan ta’adda, a fafatarwar da su ke yi, shi ne kan gaba a watan Agusta.

Wadannan ikirarin sun hada da gumurzu, tare da kisan ‘yan ta’adda, da kuma masu satar jama’a a yankin babban birnin tarayya Abuja, da shiyyoyi shida na kasar nan, da kuma karin matakan tsaro daga bangaren gwamnatocin jihohi.