Wata kotun majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti na Jihar Ekiti, ta yanke wa wani matashi mai shekara 25, Sunday Peter, hukuncin daurin wata daya a gidan gyaran hali saboda satar kifin da kimarsa ta kai Naira dubu 400.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Olubunmi Bamidele, ce ta yanke hukunci ranar Litinin, bayan wanda ake zargin ya amsa aikata laifin.
- Akwai gawarwaki 102 da ba a san danginsu ba a asibitin Abuja
- NAJERIYA A YAU: Irin Shaidar Karatu Da Ake Bukatar Masu Neman Shugabanci Su Mallaka
Sai dai ta ba wanda aka yanke wa hukuncin zabin biyan tarar Naira 10,000 ga laifin farko, sai kuma N20,000 a kan laifi na biyu.
Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Sodiq Awoniyi, ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin tare da wani mutum wanda ya cika wandonsa da iska sun aikata laifin ne ranar 16 ga watan Yunin 2022, da misalin karfe1:00 na rana a runkunin gidaje na Irewolede da ke birnin Ado-Ekiti
Dan sandan ya ce Sunday tare da daya mutumin sun hada baki wajen satar kifin samfurin catfish wanda kimarsa ta kai Naira dubu 400, mallakin wani mai suna Awe Omowumi daga wajen kiwon kifinsa.
Ya ce wanda ake zargin na farko shi ne sakataren gonar wacce mai ita ya ba shi ya rika kula da ita. (NAN)