✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar jarrabawa na ruguza al’umma —Shiek Adamu Dokoro

Ya kara da cewa kashe kasa ne zai karu kuma ilimi zai koma baya domin satar jarrabawa ba alkhairi ba ne

Sanannen malamin Musulunci a jihar Gombe, Shiek Adamu Muhammad Dokoro, ya ja hankalin dalibai musamman wadanda suke karatu a jami’a da cewa su guji satar jarrabawa domin tana ruguza al’umma.

Shiek Adamu Dokoro ya yi wannan jan hankalin ne a lokacin wani shirinsa na Ka San Addininka da ake gabatarwa a gidan Radio Progress FM da ke Gombe.

 

Ya ce wasu daliban da suke satar jarrawaba a jami’a ‘ya’yan manyan mutane ne, wadanda idan malami ya hana su sukan kai karar sa wajen iyayensu, su kuma su kai gaba cewa ana sa wa ’ya’yansi ido a lokacin jarrabawa wanda hakan yakan sa a ja kunnen malami ko a canja shi.

A cewar malamin, ko da kalibi ya kammala karatu, muddin da satar jarrabawa ya gama, ko an ba shi shaidar kammala karatunsa, ba zai yi albarla ba.

“Ku sani yin hakan ruguza al’umma ne kuma ilimin da aka masa satar jarrabawa bai ya albarka,” inji shi.

Ya kara da cewa kashe kasa ne zai karu kuma ilimi zai koma baya domin satar jarrabawa ba alkhairi ba ne.

Dokoro, ya ba da misalin yadda satar jarrabawa ke ruguza al’umma da cewa, idan da satar jarrabawa mutum ya kammala karatun likita, a karshe maimakon ya bada magani a warke sai ma dai ciwo ya karu ko a halaka majinyaci.

Hakazalika idan Injiniya ne na gini ko na hanya, hakan ke jawo yawan rushewar gine-gine.

Ya kara da cewa kashe kasa ne zai karu kuma ilimi zai koma baya domin satar jarrabawa ba alkhairi ba ne.

Mafita

Ya ce mafita ita ce dalibai su ji tsoron Allah su jajirce an yi karatu sannan a samu ilimi mai nagarta kuma mai albarka.

Daga nan kuma sai ya gargadi wasu malamai da su daina kayar da dalibai a jarrabawa musamman mata saboda neman jikinsu.