Wata Babbar Kotun Lardi dake zamanta a yankin Zuba na Babban Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa wani matashi hukuncin bulala 12 saboda satar doya.
Kotun dai ta sami Hashimu Babangida da laifin satar doyar da darajarta ta kai ta kusan N596,000.
- Sheikh Gumi ya yi wa El-Rufai raddi kan ’yan bindiga
- Mun haka wa ’yan bindiga rijiyoyi 138 —Gwamnan Zamfara
Tun da farko dai ’yan sanda sun zargi matashin wanda mazaunin Garejin Dankogi ne da laifin sata.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Gambo Garba ya shawarci matashin da ya canza halinsa.
Dan sanda mai shigar da kara, Chinedu Ogada ya shaidawa kotun cewa Hashimu ya aikata laifin da ake zarginsa ne ranar 26 ga watan Disambar 2020, bayan wanda aka yi wa satar, Tanko John ya kai kara ga ofishin ’yan sanda na Zuba.
Chinedu ya shaidawa kotun cewa Hashimu ya tsallaka gonar Tanko ne dake Zuba ya kuma sace doya ta kusan wannan adadin.
Ya ce binciken yayin binciken ’yan sanda na farko-farko, Hashimu ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma tuni aka karbe kayan satar daga hannunsa.
Laifin, a cewar dan sandan ya saba da tanade-tanaden sashe na 287 na kundin Penal Code.