Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustafa, ya ce duk da ana samun matsakaicin ci gaba a yakin da ake yi da annobar COVID-19 a Najeriya, a zahiri sassauta matakan da aka dauka na hana yaduwar cutar a Kano da ma fadin kasar ka iya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
Boss Mustapha, wanda shi ke jagorantar kwamitin yaki da annobar COVID-19 na fadar shugaban kasa y ace kwamitin na jin radadin mawuyacin halin da al’ummar kasa ke ciki, amma ba za a dauki wani mataki nan gaba ba sai idan jama’a na yin biyayya ga matakan kariya sau da kafa.
Mista Mustapha ya sanar da haka ne ranar Litinin a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar a kan annobar coronavirus.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yarda da shawarwarin da kwamitin ya ba shi na matakan rangwame da tsarin saukaka dokokin daki-daki.
“Za a ci gaba da sassauta dokar kullen da aka yi a baya zuwa makwanni biyu, daga misalin 12 na tsakar daren 18 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan 6 na shekarar 2020.
“Za kuma a kara kaimi wajen gano masu dauke da cutar tare da ba su kulawa da kuma ba da bayanai, tare da tsawaita dokar kulle a jihar Kano zuwa mako biyu.
“Bugu da kari za a sanya dokar kulle a jihohi, ko birane, ko kuma kananan hukumomin da ke da sabbin masu kamuwa da yawa idan bukatar hakan ta bijiro”, inji Boss Mustapha.
A daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta sanar da daukar wannan mataki, Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da umarnin yin sallar Idi da ta Juma’a mai zuwa bisa sharadin za a kiyaye da matakan hana yaduwar annobar.