Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin aure da aka kashe a Jihar Filato.
Tun da farko, Hakimin Basawa, Haruna Abubakar ne, ya wakilci Sarkin lokacin da lamarin ya faru, saboda Sarkin ya yi tafiya.
Sarkin, ya bayyana baƙin cikinsa bisa wannan mummunan lamari, inda ya roƙi iyalan da su ɗauki wannan a matsayin ƙaddara.
Ya yaba da yadda suka yi haƙuri kuma suka bar komai ga hukuma, ba tare da ɗaukae doka a hannunsu ba.
Sarkin ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna na ƙoƙarin ganin an bi wa waɗanda abin ya shafa haƙƙinsu.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya da haƙuri su ne mafita ga duk wata matsala, kuma hakan zai kawo ci gaba a tsakanin al’umma.
A yayin ziyarar, Sarkin ya samu rakiyar wasu daga cikin ’yan majalisarsa da hakimai.
Ya sake roƙon jama’a da su ci gaba da zaman lafiya tare da miƙa lamarin ga Allah.
Da yake magana a madadin iyalan garin, Mallam Muhammadu Dan Bami, ya gode wa Sarkin bisa ziyarar da ya kawo, tare da bayyana cewa mutanen garin masu bin doka da son zaman lafiya ne.
Daga ƙarshe, ya roƙi Sarkin da ya taimaka wajen ganin gwamnati ta cika alƙawarin da ta ɗauka na bi masu haƙƙinsu.